An yanke wutar lantarkin ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu

An yanke wutar lantarkin ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Tshwane ta Afirka ta Kudu, sakamakon bashi da ake binsu kan kudin amfani da wutar.

Babban jami’in birnin, Dr Nasiphi Moya, ya bayyana a shafin X cewa an yanke wutar ne saboda ofishin Jakadancin bai biya kudin lantarkin da ya kamata ba.

Sa’o’i kadan bayan haka, Dr Moya ya sanar cewa an dawo da wutar lantarkin.

Wannan ba shine karo y farko da bashi ya jawo yanke wutar lantarki daga ofishin Najeriya a Afirka ta Kudu ba; a watan Janairu na 2023, kamfanin rarraba wutar lantarki na City Power ya yanke wutar Jakadancin Najeriya dake Johannesburg saboda bashin dala 35,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post