Barnar Da Ke Cikin Gini A Kan Kabarburan Waliyyai (2)

Kowa ya san kasashen Musulmai cike suke da wuraren ziyara da aka gina su a kan kabarburan Shehunnai ko Waliyyai ko Imamai, aka gina Masallatai a kansu ana Sallah a cikinsu, duk da cewa; Annabi (s.a.w) ya yi hani da tsinuwa, tare da bayanin tsananin fushin Allah a kan haka, kuma aiki ne na Yahudawa da Kiristoci.

To wannan danyen aiki ya janyo manyan barna masu girma matuka ga mutanen da suka fitinu da wannan aiki, daga cikinsu akwai:

Cigaba...

11- Yin rantsuwa ma Allah da waliyyin da yake kwance a kabarin wajen addu'a. Misali mutum ya ce: na rantse da waliyyi wane Allah sai ka ba ni abu kaza.

12- Da yawan masu ziyara daga sun hango ginin da aka yi a kan kabarin waliyyin sai su fadi su yi sujuda ma waliyyin da yake kwance a kabarin.

13- Yin bakance ga waliyyin da yake kwance a kabarin, har mutum ya ware masa wani kaso daga dukiyarsa.

14- Za ka samu waliyyin da aka busne a kabarin ya fi girma a zukatansu fiye da ganin girman Allah, sun fi tsoronsa fiye da tsoron Allah. Shi ya sa da za ka nemi wani daga cikinsu  ya yi rantsuwa, to zai iya rantsuwa da Allah a kan karya ko gaskiya, amma da za ka ce ya rantse da waliyyinsa ba zai yarda ya rantse da shi a kan karya ba, saboda yadda yake tsananin tsoronsa fiye da yadda yake tsoron Allah.

15- Rokon waliyyin da ke cikin kabarin biyan bukata, da neman yaye damuwa a wajensa.

16- Kaskantar da kai a wajen kabarin waliyyin, da yin kuka, da tsayuwa cikin nitsuwa fiye da idan masallaci suka shiga suna sallah.

17- Fifita kabarburan waliyyan a kan masallatai, da fifita ibada a wurin fiye da yin ibadar a masallatai, alhali masallatan dakunan Allah ne.

18- Asali an shar'anta ziyartar makabarta ne don tuna Lahira da kuma yin addu'ar samun rahmar Allah ga mamacin, sai ya kasance sun kyautata wa kawunansu, kuma sun kyatata wa mamatan, amma sai masu bautar kabarburan suka juya lamarin, suka canza manufar ziyarar ta koma rokon mamatan, da yi musu ibada da bauta musu, sai suka haramta wa mamacin albarkar addu'o'in nasu, da rahmar Allah da zai samu a dalilin addu'o'in, kuma suka zama masu munana wa kawunansu da munana wa mamatan.

19- Cutar da mamatan ta hanyar abubuwan da suke aikatawa na bauta musu ta hanyar rokonsu biyan bukata da neman taimakonsu, da neman tsari da su, alhali waliyyan Allah na gaskiya ba za su yarda da abin da suke yi a wajen kabarburan nasu ba. Kamar yadda Annabi Isa (as) ba zai yarda da bautar da kiristoci suke yi masa ba.

20- Tsananin saba ma Allah da warware abin da ya shar'anta. Allah ya shar'anta Tauhidi ya wajabta bauta masa shi kadai, ya haramta yi masa shirka, su kuma sun zo sun warware sun sunnanta shirka, suna bauta wa waliyyai da suke kabarbura koma bayan Allah.

21- Karshe kuma duka wahalar banza suke yi, tare da zunubi mai girman gaske, wanda zai rushe musu duk wani kyakkyawa da suka aikata; imani da kyawawan aiyukansu, tare da dawwama a wuta.

Wadannan bala'i da barna masu girma duka ana samunsu ne a dalilin gini a kan kabarbura, da gina kubba a kansu.

* Daga Littafin "Taisirul Azizil Hameed" na Shaikh Sulaiman Al- Tamimiy (r).

Allah ya kiyaye mu, ya shiryi masu amsa sunan Musulmai masu wadannan aiyuka na shirka ma Allah.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post