Tattaunawa Tsakanin Mulhidi Da Dan Boko Aqeeda

Wani Mulhidi mai suna Mati Mubarak Sodangi ya kalubalanci wani Dan Boko Aqeeda mai kiran kansa Musulmi, mai suna Garba Sufiy.

Mati Mubarak ya ce: Kai Garba Sufiy, Kana karyar kai secularist ne, alhali kuma ga abin da Alkur'aninku ya ce:

{ إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِتَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ بِمَا أَرَاكَ اللَّهُ } [النساء: 105]

"Lallai mu muka saukar da Littafi gare ka da gaskiya, don ka yi hukunci tsakanin mutane da abin da Allah ya nuna maka".

To ashe a cikin Alkur'aninku aka ce a yi hukunci da Alkur'anin naku, alhali kai kuma ka zo kana cewa; hukunci da Constitution ne kawai ya dace da wannan zamani.

To kenan kai ba ka bin littafin Addinin naka kenan.

Garba Sufiy ya ce: Ai wannan a can zamanin Annabi ne ba a wannan zamanin ba.

Mati Mubarak ya ce: To a ina aka fadi haka a cikin Alkur'anin naku ko Hadisin Annabin naku?

Garba Sufiy ya ce: Ai ba sai an fadi hakan ba, saboda kowane hukunci yana dacewa ne da zamaninsa. Yanzu kuma wannan zamani bai dace da hukunci da Alkur'ani ba.

Mati Mubarak ya ce: Haba Garba Sufiy wannan abin da ka fada kowane Musulmi ya san karya kake yi.

Garba Sufiy ya yi shiru ya rasa bakin magana.

Sai Mati Mubarak ya ce: Bayan wannan kuma, kai Garba Sufiy kana karyar humanity amma a Alkur'anin da ka yarda da shi an ce a kashe kafirai, kuma a ki su a yi gaba da su. Kuma duk mai son kafirai Munafiki ne. A Kur'anin naku aka ce:

{بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (138) الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَيَبْتَغُونَ عِنْدَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا (139)} [النساء: 138، 139]

"Ka yi bushara ga Munafukai cewa; suna da azaba mai radadi. Su ne wadanda suke rikan Kafirai masoya ba Muminai ba. Shin daukaka suke nema a wajensu ne? alhali daukaka gaba dayanta ta Allah ce".

Don haka Garba Sufiy kai Munafiki ne a Musluncin naku, saboda kana cewa; kana son kafirai.

To me za ka ce a nan?

Garba Sufiy ya ce: A'a, ai su ma kafiran mutane ne, ni ba zan ki mutum ba.

Mati Mubarak ya ce: Tun da kai ka yarda da Muslunci da Alkur'ani da Allan Musulmai, to ga shi Allan ya ce kai Munafuki ne, tun da kana son kafirai.

Nan da nan sai Garba Sufiy ya fara hayaniya, yana zagin Mati Mubarak yana cewa; ai kai ba ka fahimci Alkur'anin ba.

Haka dai tattaunawar ta zo karshe, Mati Mubarak Sodangi yana so ya ja Garba Sufiy ga Addininsa na Ilhadi da kafirce ma dukkan Addinai da inkarin samuwar Allah.

To jama'a, kun ga dai yadda ta kaya, Garba Sufiy ya shiga tsaka mai wuya, shi ba Mulhidi cikakke ba, kuma ba Musulmi cikakke ba, shi ya sa Mulhidin ya tabbatar da cewa; shi Munafiki ne a cikin Musulmai.

Allah ya yi mana tsari da tabewa.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post