Kowa sai ya Buƙaci Ceton Annabi (SAW) a Lahira

Ni a yadda na fahimci maganarsa, asali ba yana nufin nuna rashin amfanin ceton Annabi (saw) ba ne, ko rashin muhimmancinsa, a'a, yana nufin cewa; shi fatansa shi ne; ya mutu yana da tarin aiyukan lada, kuma ba shi da zanubai, ta yadda ba sai ya buƙaci ceto wajen shiga Aljanna ba. Wato ceton da za a yi wa masu manyan zunubai a Lahira.

To amma ya gafala, ko ya jahilci cewa; ceton Annabi (saw) ba nau'i ɗaya ba ne, nau'uka ne har biyar.

Daga ciki, dukkan ƴan Adam za su buƙaci ceton Annabi (saw); ceton a zo a yi Hisabi. Shi ne ceto mafi girma (الشفاعة العظمى). Annabi (saw) zai ceci dukkan mutane gaba ɗaya, kowa da kowa, har Annabawa da Manzanni. A kan haka za a ba shi tutar yabo (لواء الحمد). Kowa yana ƙarƙashinta, tun daga kan Annabi Adam (as), har zuwa na ƙarshen mutane. Shi ne matsayi abin yabo (المقام المحمود) wanda Allah zai tashi Annabi (saw) a kansa, matsayin da kowa sai ya yabe shi (saw), saboda wannan ceton. Allah ya ce:

﴿عَسَىٰۤ أَن یَبۡعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامࣰا مَّحۡمُودࣰا﴾ [الإسراء ٧٩]

[Da fatan Ubangijinka zai tashe ka a matsayi sha-yabo].

Bayan wannan, zai yi ceto wa ƴan Aljanna, sai ya roƙa musu; kafin a ba su daman shiga Aljannar.

Haka kuma, daga cikin nau'o'in ceton Annabi (saw) a Lahira, akwai ɗaga darajojin ƴan Aljanna a cikin Aljannar. Wato idan mutum yana daraja ta biyar - misali; yana beni hawa na biyar -, sai Annabi (saw) ya cece shi, sai a ɗaga darajarsa zuwa hawa na goma.

To ka ga babu wanda zai san wannan, sai kuma ya ce: ba ya buƙatar ceton Annabi (saw).

To amma me ya kai shi ga wannan kuskuren?

A gaskiya a cikin shekarun nan, matasa Ahlus Sunna suna ta faɗawa ramuka a dalilin jayayyarsu da ƴan bidi'a Sufaye. Da sunan yaƙar ƴan bidi'a, su ma suna faɗawa cikin wasu bidi'o'in.

Da ma haka yake faruwa, idan mutum bai tsayu a kan Sunna sosai ba, ko ya jahilce ta, bai santa da kyau ba, to a wajen rigima da ƴan bidi'ar shi ma zai faɗa wasu bidi'o'in.

A dalilin bidi'ar ƴan "Wa'eediyya" (Khawarijawa da sauransu) aka samu bidi'ar "Murji'a".

A dalilin bidi'ar Rafidha ƴan Shi'a aka samu bidi'ar "Nasibawa".

A dalilin bidi'ar ƴan "Ƙadariyya" aka samu bidi'ar "Jabariyya".

Da ma abin da yake janyo haka shi ne watsi da Alƙur'ani da Sunna da tafarkin Salaf, da bin son zuciya.

Haka kuma a dalilin jayayya da ƴan bidi'a da husuma da su, ana ɗiban bidi'o'i. Shi ya sa yana daga cikin Ƙa'idojin Ahlus Sunna masu muhimmanci, nisantar husuma da jayayya a Addini, kamar yadda Imamu Ahmad ya nassanta a farkon littafin "Usulu al-Sunna" (أصول السنة).

Wannan ya sa Malaman "Ilmul Kalam" da suka shagaltu da jayayya da ƴan Falsafa, ba tare da aiki da Alƙur'ani da Sunna ba, sai suka afka cikin babbar Bidi'a, Bidi'ar "Ilmul Kalam", wacce suka rushe Aƙidun Muslunci da shi.

To wannan shi ne abin da yake faruwa. Akwai wasu matasa a wannan zamani, ba su yi karatu sosai ba, amma saboda arahan kafar isar da saƙo (social media), sun bayyana kawunansu, mutane sun naɗa su a matsayin Malamai, alhali ba Malamai ba ne. Wannan ya sa suke sakin baki, suke ɓarin magana, suke faɗin maganganun da suke janyo hayaniya, don su ja hankulan mutane gare su, don neman mabiya. Musamman saboda akwai kafafen da idan kana da mabiya masu yawa, kuma suna bibiyarka, to za kana samun kuɗi.

Bayan haka kuma, dambarwar da take faruwa tsakanin Sufaye ƴan bidi'a da Ahlus Sunna a kan matsayin Annabi (saw), wasu matasan suna sakaci da matsayin Annabi (saw), suna sakaci wajen girmama Annabi (saw) da sunan kira ga Tauhidi. Alhali - Wallahi - Tauhidi ba ya rabuwa da girmama Annabi (saw).

Kamar yadda Tauhidi yake Wajibi mafi girma, haka girmama Annabi (saw) yake Wajibi mai girma. Ba za ka rabauta ba sai ka haɗa su duka biyu. Don haka dole mu lazimci ladabi yayin faɗin maganar da ta shafi Annabi (saw). Ladabi na Shari'a, ba na guluwwin ƴan bidi'a ba.

Don haka, ko shakka babu, irin lafuzan da muke ji a cikin kwanakin nan, da sunan raddi ga Sufaye ƴan bidi'a, ko ba su haushi, lallai akwai rashin girmama Annabi (saw) a cikinsu. Kamar cewa; ba a buƙatar ceton Annabi (saw).

Ala ayyi halin, duk wanda zai yi Addini don ba da haushi wa ƴan bidi'a, to ya rinƙa afkawa cikin miyagun Aƙidu, da furta munanan maganganu, musamman a haƙƙin Annabi (saw).

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post