Dalili Na Hankali A Kan Cancantar Allah Ga Bauta Shi Kadai

A cikin Alkur'ani Allah ya kafa hujja da dalilai na hankali masu yawa a kan cancantarsa ga bauta shi kadai, ta hanyar bayyana rashin cancantar sauran ababen bauta. Misalai a kan haka suna da yawa, daga ciki; ya zo a kissar mutanen Annabi Musa (saw) da aka kera musu dan maraki suke bautawa, Allah ya ce:

{فَأَخْرَجَ لَهُمْ عِجْلًا جَسَدًا لَهُ خُوَارٌ فَقَالُوا هَذَا إِلَهُكُمْ وَإِلَهُ مُوسَى فَنَسِيَ (88) أَفَلَا يَرَوْنَ أَلَّا يَرْجِعُ إِلَيْهِمْ قَوْلًا وَلَا يَمْلِكُ لَهُمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا (89)} [طه: 88، 89]

Ma'ana: shin ba sa ganin in sun yi magana ga dan marakin ba ya iya mayar musu, kuma ba ya iya amfana musu komai, ba ya iya cutar da su da komai, amma a hakan ya zama abin bauta?

Duk mai hankali ya san cewa; mai magana, mai amfanarwa da cutarwa shi ne ya cancanci bauta, ba wanda ba ya iya yin hakan ba.

Kuma duk cikin ababen bauta babu mai siffofin kamala, kamar sifar magana da cikan ilimi, kuma yake amfanarwa da cutarwa da amsa addu'a da biyan bukatun masu rokonsa sai Allah shi kadai, don haka shi kadai ya cancanci a bauta masa, ba tare da hada shi da abokin tarayya ba.

Da wannan za ka fahimci wautar masu zuwa kabarin Shehu suna rokonsa biyan bukata, haka 'Yan Shi'a da suke zuwa kabarin Imam suna rokonsa, alhali ba sa jinsu, kuma ba za su iya mayar musu jawabi ba, kuma ba su mallaki komai ba, balle su iya biya musu bukata,

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post