Ahlus Sunna Gaskiya Kawai Suke Bi Ba Ta'assubanci Ga Wani Malami Ko Wata Kungiya Ba

Yana daga cikin fitinar da Ahlus Sunna suke fama da ita a wasu wuraren na rabuwa zuwa bangarori daban - daban, jama'a daban - daban, kowane bangare suna alfahari da abin da suke da shi. Wanda wannan ya sa jama'ar Ahlus Sunna suna ta kara rabuwa kashi - kashi, suna raya ta'assubanci da kungiyancin da Allah da Manzonsa suka yi hani a kai. Alhali abin da Allah ya wajabta mana kuma Manzon Allah (saw) ya zo mana da shi shi ne; BIN GASKIYA DA KARBANTA DAGA WAJEN KOWA, SAWA'UN MASOYI NE KO MAKIYI. ZABE WAJEN KARBAN GASKIYA, KARBANTA DAGA WANDA AKE SO, DA KINTA DAGA WANDA AKE KI, WANNAN SHI NE KUNGIYANCI DA TA'ASSUBANCI DA BIN SON RAI WANDA NASSOSHI MASU YAWA SUKA ZO A CIKIN AL- QUR'ANI DA SUNNA SUNA ZARGIN MAI AIKATASU.

Al- Allama Ibnu Qayyimil Jauziyya (r) ya ce:

فمن هداه الله سبحانه إلى الأخذ بالحق حيث كان، ومع من كان، ولو كان مع من يبغضه ويعاديه، ورد الباطل مع من كان، ولو كان مع من يحبه ويواليه، فهو ممن هدي لما اختلف فيه من الحق. فهذا أعلم الناس وأهداهم سبيلا وأقومهم قيلا.

"Duk wanda Allah ya shirye shi ga karban gaskiya a duk inda take, kuma a tare da kowaye ne, ko da kuwa tana tare ne da wanda yake ki ne, kuma yake gaba da shi, da kuma jefar da karya da take tare da kowaye, ko da kuwa tana tare ne da wanda yake so, kuma yake jibintarsa, to wannan yana cikin wanda aka shiryar da shi ga abin da aka yi sabani a kansa na gaskiya. Wannan shi ne mafi ilmi a cikin mutane kuma mafi shiriyansu zuwa ga kyakkyawar hanya, da mikakkiyar magana".

Duba Al- Sawa'iq 2/ 516.

Abin Lura:

1. Gaskiya kawai ake bi a duk inda take, da kowaye take tare.

2. Ta'assubanci da Kungiyanci shi ne zaban wani mutum, ko wata jama'a, wajen bin maganarsa, kawai don kana sonsa kana tare da shi. Sa'awa'un yana tare da gaskiya ko ya kauce ma gaskiyar.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

16 December, 2013

Shin akwai Son Annabi (saw) a cikin Alƙur'ani?

Idan a da ba ka fahimci dalilin da ya sa Salaf suke kiran ƴan Bidi'a da sunan "أهل الأهواء", "Ahlul Ahwa'i" (masu son zuciya) ba, to na tabbata a wannan zamanin za ka fahimci dalilin, saboda yadda son zuciyar ƴan bidi'a ya bayyana a fili, a dambarwan da ake yi a wannan lokaci.

A yau idan ina magana da ɗan-tatsine, sai na ce: in ya isa, ya kawo min Ayar da ta ce: A so Annabi (saw).

Umurni "sarihi".

Duk mai adalci - wanda ba shi da son zuciya - to ba zai fitar da maganar daga "siyaƙinta" ba. Ma'ana; ba zai ɗauki maganar a sake ba, zai barta a yadda take, a matsayin ƙalu-bale aka jefa ma wanda ba ya aiki da komai, sai umurnin da ya zo cikin Alƙur'ani kaɗai.

Kuma kowa ya san cewa; babu yadda za a yi ɗan tatsine ya iya kawo Ayar.

Amma sauran ƴan bidi'a, ƴan son zuciya, don su samu dalilin ƙara kafirta Bawahabiye, da cewa; ba ya son Annabi (saw), zai ɗauki maganar a sake, a matsayin Bawahabiye yana kore umurni da son Annabi (saw) a cikin Alƙur'ani!

To ka ga wannan son zuciya ne da zalunci, daga ƴan Bidi'a, "أهل الأهواء", "Ahlul Ahwa'i" (ƴan son zuciya)!

Ya zaɓi ya yi ɓatanci wa Bawahabiye, a kan a yi ilzami wa ɗan tatsine, a rushe Aƙidarsa, ba don komai ba sai saboda son zuciya!

Ɗazu na ji wani ɗan bidi'a, ɗan Ɗariƙa, -wai- shi a dole ya kama Bawahabiye yana kore umurnin son Annabi (saw) a Alƙur'ani, yake cewa:

Bai san cewa:

"الخبر يأتي بمعنى الإنشاء، ويفيد الأمر" ba.

Yana nufin Ayar cikin Tauba:

(أحب إليكم من الله ورسوله)

To, ya kai ɗan son zuciya, kar ka manta; wannan abin da ka faɗa, ƙa'idar da ka kawo, a wajen ɗan tatsine sunansa: "ƙala ƙato", wato maganar ƙaton banza ne. Don haka ba zai karɓa ba. Shi kawai Alƙur'ani zalla ya yarda da shi.

Saboda haka wannan ƙalu-bale da aka jefa wa ƴan tatsine, yana nan a tabbace daram. Don haka a Aƙidar ƴan tatsine; Allah bai yi umurni da son Annabi (saw) ba, tun da babu umurni "sarihi" a kan haka, a cikin Alƙur'ani. To ta yaya son Annabi (saw) zai zama wajibi a gurinsu?

Don haka ƴan bidi'a "أهل الأهواء", "Ahlul Ahwa'i" (masu son zuciya), ba ku isa ku ƙwaci ƴan tatsine a hanun Mabiya Annabi (saw), masoyansa na gaskiya ba.

Allah ya raba mu da son zuciya.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post