Abin takaici, akwai da yawa daga cikin masu dangantuwa ga Muslunci wadanda suke afkawa cikin Shirka da Bidi'a, imma saboda jahilci da kawar da kai ga koyon Addini da neman iliminsa, ko saboda son zuciya da neman abin Duniya na dukiya da mata'in rayuwa da daukaka da son shugabanci.
Daga cikin manyan abubuwa da suke nuna hatsarin Shirka da
Bidi'a akwai kasancewar Shirka rena Allah ne da kaskantar da shi da tauye
hakkinsa da rashin girmama shi. Kamar yadda Bidi'a kuma take lazimta rena
Annabi (saw) da kaskantar da shi, da rashin girmama shi.
Al-Allama Ibnul Qayyim ya ce:
الشرك
ملزوم لتنقص الرب سبحانه، والتنقص لازم له ضرورة، شاء المشرك أم أبى، ولهذا اقتضى
حمده سبحانه وكمال ربوبيته أن لا يغفره، وأن يخلد صاحبه فى العذاب الأليم، ويجعله
أشقى البرية. فلا تجد مشركا قط إلا وهو متنقص لله سبحانه، وإن زعم أنه يعظمه بذلك.
كما أنك لا تجد مبتدعا إلا وهو متنقص للرسول صلى الله تعالى عليه وآله وسلم، وإن
زعم أنه معظم له بتلك البدعة. فإنه يزعم أنها خير من السنة وأولى بالصواب، أو يزعم
أنها هى السنة، وإن كان مستبصرا فى بدعته فهو مشاق لله ورسوله.
فالمتنقصون
المنقوصون عند الله تعالى ورسوله وأوليائه: هم أهل الشرك والبدعة ولا سيما من بنى
دينه على أن كلام الله ورسوله أدلة لفظية لا تفيد اليقين، ولا تغنى من اليقين
والعلم شيئا.
إغاثة
اللهفان من مصايد الشيطان (1/ 62 - 63)
"Shirka tana lazimta kaskanta Allah Ubangiji Tsarkakakke
da rashin girmama shi, dole Shirka ta lazimta kaskanta Allah, sawa'un Mai
shirkan ya ki ko ya so. Saboda haka ne daukakar Siffofin Allah da kamalar
Rububiyyarsa suka hukunta cewa; Allah ba zai gafarta Shirka ba, kuma zai
dawwamar da mai yinsa a cikin azaba mai radadi, kuma zai sanya shi ya zama bawa
mafi rashin rabo. Saboda haka ba za ka taba samun Mushriki ba face yana
kaskanta Allah Tsarkakakke, ko da kuwa yana raya cewa; yana girmama shi.
Kamar yadda ba za ka taba samun Dan Bidi'a ba face yana mai
kaskanta Manzon Allah (saw), ko da kuwa yana raya cewa; shi mai girmama shi ne
da Bidi'ar tasa. Saboda ai yana raya cewa; Bidi'ar ta fi Sunna, kuma ta fi
cancantar samun lada, ko yana raya cewa; Sunna ce, in kuma ya kasance masani ne
a kan Bidi'ar tasa to shi mai saba ma Allah da Manzonsa ne.
Saboda haka, makaskanta masu kaskanta Allah da Manzonsa a wajen
Allah da Manzonsa da Waliyyansa su ne Masu Shirka da Masu Bidi'a, musamman
wanda ya gina Addininsa a kan cewa; Maganar Allah da Manzonsa zato ne ba yakini
ba, ba sa samar da yakini da ilimi".
Wannan ya sa 'Yan Bidi'a suke fada da Maganar Allah da Manzonsa
(Ayoyi da Hadisai), suke Tawilin Ayoyi, da gangan su fitar da su daga
zahirinsu, su soke Hadisai su zubar da su, saboda babu abin da yake rushe
Bidi'a kamar Nassoshin Shari'a. Shi ya sa suke da damuwa game da Nassoshin
Shari'a a zukatansu.
Shi ya sa ya ce:
لا
تجد مبتدعا في دينه قط إلا وفي قلب حرج من الآيات التي تخالف بدعته
الفوائد
لابن القيم (ص: 82)
"Ba za ka samu Dan Bidi'a a Addininsa ba face yana jin
kaikayi da damuwa a cikin zuciyarsa game da Ayoyin da suka saba
Bidi'arsa".
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani