Haka duk Da'awar da babu tausayin wanda kake kira da tausasa masa, kuma babu ihtiraminsa, to ba Da'awa ba ce. Saboda Da'awa kiran mutane ne, su zo su saurara, su fahimta, su amsa, su karɓa, to idan ba ka tausaya ma wanda kake kira, ka tausasa masa, ka yi ihtiraminsa ba, to ta yaya wannan zai zama kira (Da'awa)?!
Ai wannan koran mutane ne ba kiransu ba!
Ginshiƙan Da'awa uku ne; Ilimi, tausasawa (الرفق) da kuma haƙuri.
A yau idan ka duba masu magana da sunan masu Da'awa - musamman
matasa -, za ka ga ba su da rabo a cikin waɗannan siffofi, waɗanda su ne
ginshiƙan Da'awar Annabawa.
Ilimi da Da'awa duka biyu ibada ne, akwai yadda ake yinsu, ba
kawai mutum zai yi yadda ya ga dama ba ne. Alƙur'ani da Sunna da Sirar Annabi
(saw) cike suke da bayanin haka.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Nisa daga Allah mataki-mataki ne, wanda sabonsa ya fi girma ya
fi nisa da Allah. Haka wanda ya fi yawaita sabon Allah ya fi nisa daga Allah
fiye da wanda ba ya yawaitawa.
Al-Allama Ibnul Qayyim (ra) ya ce:
والبعد
من الله مراتب بعضها أشد من بعض. فالغفلة تبعد العبد عن الله، وبعد المعصية أعظم
من بعد الغفلة، وبعد البدعة أعظم من بعد المعصية، وبعد النفاق والشرك أعظم من ذلك
كله.
الجواب
الكافي ط عالم الفوائد (1/ 191 - 192)
"Nisa daga Allah mataki-mataki ne, wani ya fi wani girma a
cikinsu. Gafala (rashin ambaton Allah da mantawa da shi) tana nisantar da bawa
daga Allah, nisan da aikata sabo yake haifarwa tsakanin bawa da Allah ya fi
girma fiye da nisan da Gafala take haifarwa, nisan da Bidi'a take haifarwa
tsakanin bawa da Allah ya fi girma fiye da nisan da aikata sabo yake haifarwa,
nisan da Munafurci da Shirka suke haifarwa tsakanin bawa da Allah ya fi girma
fiye da sauran dukkansu".
Bayin Allah, ya wajaba mu tsoraci dukkan abin da zai nisanta mu
da Ubangijinmu Mahaliccinmu Mai renonmu, Mai arzurta mu, Mai gudanar mana da
lamuranmu, Mai biya mana bukatunmu.
A kullum mu zama masu ambaton Allah ta hanyar yi masa zikiri da
tuba gare shi, da yi masa da'a ta hanyar kiyaye Farillai da aikata Mustahabbai.
Mu guji abubuwa da za su nesanta mu daga Allah Mai rahama, ta
hanyar saba masa da karya dokokinsa da fita daga Shari'arsa. Mu nisanci, gafala
da sabo, mu kiyayi Bidi'o'i na Aqidu da aiyuka, balle kuma Shirka, Shirka tana
hana shiga Aljanna gaba daya. Bare kuma Munafurci, abin da yake dawwamar da
mutum a cikin Wuta a kasan Kafirai.
Ya Allah ka kubutar da mu, ka yafe mana sakacinmu, ka gafarta
mana zunubanmu.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani