Ƴan Bidi’a suna suka tara, ba a layin daya suke ba. Akwai yan bidi’an da bidi’arsu ta kafirci ce. Akwai kuma yan bidi’ar da bidi’arsu ba ta kai kafirci ba, wato ta fasiƙanci ce. To tunda ba a matsayi ɗaya suke ba, to hukuncinsu ma ba ɗaya yake ba.
Na farko:
Su yan Bidi’a ta kafirci su ne; duk wanda yake amsa sunan
Musulmi, amma yana shirka ma Allah, yana zuwa kabarburan waliyyai yana roƙonsu
biyan buƙata, ko wani nau'i cikin nau’ukan babbar shirka.
Ko kuma wanda yake amsa sunan Musulmi, amma yana da Aƙida ta
kafirci; Aƙidun Zindiƙai Munafukai, kamar Aƙidar "Wahdatul Wujudi"
(Aƙidar komai Allah ne), da sauran miyagun Aƙidu na kafirci, waɗanda mai su
Zindiƙi ne Munafuki.
To mai wannar sifa da ta gabata, wato mai bidi'a ta kafirci,
bai halasta a nema masa rahma da gafara ba idan ya mutu. Saboda Allah ya
haramta nema wa Mushrikai da Munafukai gafara. Allah ya ce a game da Mushrikai:
{مَا
كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ
وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ
أَصْحَابُ الْجَحِيمِ} [التوبة: 113]
{113. Bai kamata ba ga Annabi da waɗanda suka yi imani su nema
wa mushrikai gafara, ko da kuwa sun kasance dangi ne na kusa, bayan kuwa ya
riga ya bayyana gare su cewa lalle su ƴan wuta ne}.
A game da Munafukai kuma ya ce:
{اسْتَغْفِرْ
لَهُمْ أَوْ لَا تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ إِنْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ سَبْعِينَ مَرَّةً
فَلَنْ يَغْفِرَ اللَّهُ لَهُمْ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ
وَرَسُولِهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ} [التوبة: 80]
{80. Ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu gafara ba (duk ɗaya
ne). In da za ka nema musu gafara sau saba’in to Allah ba zai gafarta musu ba.
Wannan kuwa saboda sun kafirce wa Allah da Manzonsa. Allah kuwa ba Ya shiryar
da mutane fasiƙai}.
Kuma ya ce:
{سَوَاءٌ
عَلَيْهِمْ أَسْتَغْفَرْتَ لَهُمْ أَمْ لَمْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ لَنْ يَغْفِرَ
اللَّهُ لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ} [المنافقون:
6]
{6. Duk ɗaya ne game da su, ka nema musu gafara, ko ba ka nema
musu gafara ba, Allah ba zai gafarta musu ba har abada. Lalle Allah ba Ya
shiryar da mutane fasiƙai}.
Saboda haka, duk mai amsa sunan Musulmi, amma yana shirka ma
Allah, ko yana da wata Aƙida ta kafirci, cikin Aƙidun Zindiƙai Munafukai, to
haramun ne a nema masa rahma da gafara idan ya mutu.
To amma a nan dole ne a tabbatar da kafircin nasa bisa yaƙini,
ba zato da kokonto ba. Don haka dole a tabbatar da abubuwa biyu:
1- Dole sai an tabbatar yana da Aƙidar kafircin ta hanyar
furucinsa da zantukansa ko kuma a aikace, ya kasance an ga kafirci da shirkan a
aikace bisa tabbas yana aikatawa.
2- Kasancewarsa yana wata ƙungiya ta bidi’a mai Aƙidun kafirci
ba zai wadatar ba.
Ma'ana; don ya kasance Rafidhi Ɗan Shi’a, ko ya kasance Ɗan
Tijjaniyya ba zai wadatar ba, dole sai an tabbatar yana furta Aƙidun kafircin,
ko yana aikata aiyukan kafircin; na shirka da sihiri da bokanci da sauransu.
Don haka ba a hukunci a kan Addinin mutane da zato da
kame-kame, dole sai dai a gina shi bisa yaƙini.
Na biyu:
Sai Ɗan Bidi’a mai bidi’a ta fasiƙanci. Shi kam wannan ya
halasta a nema masa rahma da gafara, saboda bidi’arsa ba ta kai ga kafirci ba.
Amma sai dai idan ya kasance mai kira ne zuwa ga bidi'ar tasa,
to ba a so manyan mutane cikin Malamai da waɗanda ake koyi da su a Addini su
nema masa rahma da gafaran a bayyane, sai dai a ɓoye, don kada mutane su yi
sakaci da bidi’ar tasa, su ɗauka lamarinsa mai sauƙi ne.
Wato kamar yadda ba a so irin waɗannan manyan mutanen su
halarci jana’izarsa, haka ba a so su nema masa rahma da gafaran a bayyane,
saboda hukuncin nema wa ƴan Bidi’a rahma da gafara a haɗe yake da hukuncin yi
musu Sallar jana’iza.
Na uku:
Haka wanda ba a san yanayinsa ba, ko ana shakka a kansa, shin
bidi’arsa ta kafirci ce ko a fasiƙanci?
Shi ma wannan ya halasta a nema masa rahma da gafara, saboda
babu yaƙini a kan bidi'ar tasa ta kafirci ce.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani