Hakki mafi girma a kan bayi shi ne hakkin Allah Madaukaki.
Daga cikin hakkokin Allah a kan bayi akwai:
1- Mu bauta masa shi kadai, mu kadaita shi da bauta, kar mu hada shi da komai cikin bauta, tare da tsarkake bautar gare shi shi kadai ta hanyar Ikhlasi.
2- Mu san cewa; shi ne Ubangijin kowa da komai, shi ne
mamallaki mahalicci shi kadai, shi ne mai arzurtawa, mai amfanawar da cutarwa,
babu abin da ke fita daga cikin mulkinsa da halittarsa da ikonsa da ganin
damansa da gudanarwansa. A wajensa ake rokon samun amfani, kuma ake neman tsari
daga cutarwa.
3- Mu tabbatar masa dukkan abin da ya tabbatar ma kansa na
sunaye kyawawa da siffofinsa na kamala da daukaka. Wadanda suke kyawawa wadanda
suka kai matuka wajen kyau.
4- Mu tsarkake shi daga dukkan abin da ya tsarkaka daga gare
shi, ya tsarkaka daga kishiya a halitta da mulki, ya tsarkaka daga abokin
tarayya cikin bauta, ya tsarkaka daga misali ko makamanci a cikin sunayensa da
siffofinsa. Ba shi da madaidaici a cikin halittarsa da sunayensa da siffofinsa.
5- Mu bauta masa ta hanyar Shari'ar da ya saukar a cikin
littafinsa, kuma ya yi wahayinta ga Manzonsa (saw), ba ta hanyar bidi'a da
surkulle da almara ba. Mu yi imani da dukkan abin da ya umurce mu da yin imani
da shi, mu yi aiki da Shari'arsa a dukkan rayuwarmu.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani