Hari Da Isra’ila Ta Kai Ya Bugi Makarantar Yan Mata A Minab, Iran; Akalla Mutane 53 Sun Mutu

 Wani hari da ake dangantawa da Israel ya afkawa wata makarantar firamare ta ‘yan mata a birnin Minab, a lardin Hormozgan Province na kudancin Iran, inda aƙalla mutane 53 suka mutu, a cewar kafafen yaɗa labaran gwamnati.

Hormozgan Province

Rahotanni sun ce harin ya faru ne yayin da ake tsaka da darasi, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama, ciki har da yara kanana. Kungiyoyin agajin gaggawa sun garzaya wurin domin ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzai, yayin da ake ci gaba da tantance yawan wadanda suka jikkata.

Hukumomin Iran sun yi kakkausar suka kan harin, suna zargin Isra’ila da kai hari kan fararen hula. Sun bayyana lamarin a matsayin babban cin zarafi da kuma karya dokokin kasa da kasa.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake samun musayar hare-hare da barazanar kara fadada rikici tsakanin bangarori daban-daban.

Post a Comment

Previous Post Next Post