Samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, wanda aka fi sani da 'solar' na ci gaba da samun karɓuwa a ƙasashen Afirka masu tasowa, inda ake fama da ƙarancin lantarki.
A Najeriya lamarin ya zama ruwan dare a sassan Najeriya sakamakon rashin tabbas ɗin samun lantarki daga babban layin wuta na ƙasar.Fiye da mutane miliyan 80 na fuskantar rashin wutar lantarki a sassan Najeriya, kuma ko waɗanda ke da wutar ma suna fuskantar katsewarta akai-akai.
Wani bincike na Energy Tracker a shekarar 2024 ya ce Najeriya na da kusan megawatt 385.7 na makamashin hasken rana, bayan da ta ƙara da megawatt 63.5 a shekarar, abin da ya sa ƙasar ta zama ta huɗu a nahiyar Afirka wajen amfani da makamashin hasken rana.
Amma a tatare da wannan ci gaba da ake samu akwai bukatar samun ingantattun bayanai kan irin matakan kiyayewa hadurra da za a iya amfani da su domin kare kai daga bala'o'i da kan iya tasowa sanadiyyar amfani da tsarin, wanda ke ci gaba da samun karɓuwa.
A baya-bayan nan an riƙa zargin akwai yiwuwar wutar sola ce ta haifar da gobara a kasuwar Singa da ke Kano, inda aka yi asarar dukiya mai ɗimbin yawa, duk da dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.