Mutane 100,000 Sun Yi Sallah A Masallacin Al-Aqsa Duk Da Takunkumin Isra’ila A Juma’a Ta Biyu Ta Ramadan

 Kimanin Falasɗinawa 100,000 ne suka halarci sallar Juma’a a harabar Al-Aqsa Mosque, duk da tsauraran matakan tsaro da Isra’ila ta kafa a Juma’a ta biyu cikin watan Ramadan.

Al-Aqsa Mosque compound

Hukumomin Israel sun tura jami’an tsaro da dama a cikin tsohon birnin Kudus, tare da kafa shingaye da takaita shiga ga masu ibada daga West Bank. Wasu Falasɗinawa sun ce an hana su wucewa ko kuma sun dauki lokaci mai tsawo a wuraren bincike.

Isra’ila ta ce matakan tsaron sun zama dole domin tabbatar da zaman lafiya, musamman a watan Ramadan lokacin da dubban masu ibada ke taruwa a wurin mai tsarki.

Sai dai ga Falasɗinawa, samun damar shiga Masallacin Al-Aqsa,  wuri mai tsarki na uku a Musulunci, na da muhimmanci ta fuskar addini da siyasa. Takaita shiga a irin wannan lokaci kan haddasa fushi da kuma kara tsananta rikici a yankin.

Duk da takunkumin, dubban mutane sun cika harabar masallacin domin gudanar da ibada, abin da wasu ke gani a matsayin nuna jajircewa da tsayin daka.

Post a Comment

Previous Post Next Post