Pakistan Ta Kai Hari Kabul: Me ya sa Afghanistan Da Pakistan Ke Fada?

 Rikici tsakanin Pakistan da Afghanistan ya sake ɓarkewa, lamarin da ya jawo fargaba a yankin. Dangantakar ƙasashen biyu ta daɗe tana fuskantar matsaloli saboda batutuwan tsaro, iyaka da kuma ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Tehreek-e-Taliban Pakistan

Babban abin da ke haddasa rikicin shi ne zargin da Pakistan ke yi cewa wasu kungiyoyin ‘yan bindiga, musamman Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), suna amfani da ƙasar Afghanistan a matsayin mafaka domin kai hare-hare cikin Pakistan. Sai dai hukumomin Afghanistan suna musanta wannan zargi, suna kuma cewa hare-haren da Pakistan ke kaiwa sun saba wa ikon ƙasarsu.

Wani muhimmin dalili shi ne takaddamar iyakar da ake kira Durand Line, wadda aka shimfiɗa tun zamanin mulkin mallaka a shekarar 1893. Pakistan na kallon ta a matsayin iyakar hukuma ta ƙasa da ƙasa, amma Afghanistan ta dade tana nuna rashin amincewa da ita. Gina katanga da wuraren bincike a kan iyakar ya sha haddasa arangama tsakanin sojojin kasashen biyu.

Har ila yau, batun korar ‘yan gudun hijirar Afghanistan daga Pakistan ya kara dagula al’amura. Pakistan ta ce matakin ya zama dole saboda matsalolin tsaro da tattalin arziki, yayin da Afghanistan ke ganin hakan na kara jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Ko da yake ba a sa ran rikicin zai rikide zuwa cikakken yaki ba, ci gaba da rashin yarda da juna da kuma musayar hare-hare na barazana ga zaman lafiya a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post