𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. A watannin baya muna wasa da mijina sai ya ce: ‘Kar fa ki bari matata ta gan ki kina riƙe mini hannu!’ Na ce: ‘Kana nufin ni ba matarka ba ce?’ Wannan duk wasa ne, domin na san ba shi da wata matar. Amma matsalar ita ce: Yanzu da na tuntuɓe shi a kan matsayin amsar da nake tsammanin ya ba ni a lokacin cewa: ‘E, ke ba matata ba ce!’ Sai ya nuna shi bai tuna an yi hakan ba! To, malam yaya zan yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
A irin wannan halin abin lura dai shi ne: Abin da shi mijin ya
furta ko ya aikata, ba abin da matarsa ta faɗa ko ta aikata ko kuma take
tunanin mijin ya aikata ba. Domin sakin aure a hannun miji ne shari’a ta ɗora
shi, ba a hannun mata ba. (Surah Al-Baqarah: 231-232; 236-237)
Shi kuma mijinki kin ji, bai tuna ma an yi hakan ba. Kuma ke
kanki ma ba ki tabbatar da cewa ya faɗi abin da kike tunanin ya auku ɗin ba.
Sannan kuma a ƙa’ida ko da abin ya auku daidai yadda kika furta
ne, to sai dai ya zama saki ne na Kinaya, amma ba saki Sarihi ba. Shi kuwa saki
na Kinaya ba a zartar da shi in ji malamai, sai a bayan an ji manufar wanda ya
furta shi.
Don haka dai a nan babu wani abin da za ki yi sai dai ki kiyaye
yi wa mijinki irin wannan wasan da irin wannan tambayar a nan gaba, don kar ya
furta miki sakin a fili ƙarara.
Allah ya kikaye.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
