Sweden Ta Tabbatar Da Kama Jirgin Ruwa Mara Matuki Na Rasha Kusa Da Jirgin Yakin Faransa

 Hukumomi a ƙasar Sweden sun tabbatar da cewa an tare wani jirgi mara matuƙi na Russia kusa da wani jirgin ruwan yaƙi na Faransa da ke gudanar da aiki a yankin.

Hukumomi a ƙasar Sweden

Rahotanni sun nuna cewa an gano jirgin mara matuƙin yana shawagi a kusa da jirgin ruwan kafin a bi diddigin sa tare da daƙile shi. Ana kyautata zaton jirgin ruwan da abin ya shafa shi ne French aircraft carrier Charles de Gaulle, wanda ke cikin atisayen soji da ayyukan tsaro a teku.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin Rasha da kasashen Yamma kan batutuwan tsaro da zirga-zirgar soji a yankin Turai.

Hukumomin tsaron Sweden sun ce an shawo kan lamarin ba tare da karin rikici ba, amma masana sun ce irin wadannan abubuwa na nuna yadda yanayin tsaro ke da sarkakiya a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post