Anka ta ɗan baƙo mai wuyar kai yaƙi, mai gari kusa ga ruwa
Wannan ☝️shi ne kirarin garin Anka, hedikwatar masarautar Anka, Jihar Zamfara, Nijeriya inda daga nan ne shugaban majalisar masarautun Jihar Zamfara, Mai martaba Sarkin Zamfara Anka, Alh. Muhammad Attahiru Ahmad CON yake gabatar da jagorancin wannan majalisa.
Duk da rashin samun taƙamaiman lokacin da aka kafa wannan gari na Anka, babu tababa Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ne maƙirƙirin wannan gari mai ɗimbin tarihi da tasiri a rayuwar Zamfarawa ya zuwa yau. Sanin ko wane ne wannan bawan Allah kuma wani batu ne mai zaman kansa da za a tattauna akai zuwa gaba In Shaa Allah.
Kiran Anka da inkiyar "ta Ɗan Baƙo " da kuma " mai gari kusa da ruwa" ba zai rasa nasaba da yadda wannan birni ya fita daga hannun Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau zuwa ga Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ba, wanda ya soma sarautar Daular Zamfara a garin Sabongari/Sabongarin Damri dake cikin Masarautar Bakura, Jihar Zamfara ta yanzu a shekarar 1815.
Ana kuma hasashen Koguna biyu da suka zagaye garin ta gabas da yamma wato Kogin Zamfara da Kogin Ka ne dalilin kiran Anka da "mai gari kusa ga ruwa". Allahu Wa'alam!
Anka ta yi wuyar akai mata yaƙi domin tun bayan shigowar Sarkin Zamfara Ɗanbaƙo a shekarar 1815 har zuwa 1903 da Turawan mulkin mallaka na Ingila da suka ci Daular Usmaniyyah babu wani gamsasshen bayani dake nuna a sake mamaye Zamfarawa har ma su rasa hedikwatarsu.
Bayan ɗauke hedikwatar Daular Zamfara daga Dutci/Dutsi (Dutsi hedikwatar gunduma ce a Masarautar Zurmi, Jihar Zamfara) da Sarkin Zamfara na 7, Sarki Bakurukuru ɗan Dakka ya yi a cikin 1300 zuwa inda ya ƙirƙira wato Birnin Zamfara dake cikin gundumar Isa, Jihar Sokoto zuwa lokacin mulkin Sarkin Zamfara Maroƙi (1754-1764 ko 1764 zuwa 1779) da ya fafata da Gobirawa, abun da ya yi sanadiyar tasowarsa daga Birnin Zamfara zuwa Banga(a cikin Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara) inda ya kafa sabuwar hedikwatarsa, zuwa mulkin Sarkin Zamfara Ɗan Bawa ɗan Gado(1804-1805) da ya yi mulki a Kuryar Madaro( a cikin Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara) zuwa mulkin Sarkin Zamfara Abarshi ɗan Maroƙi(1805-1815) da ya yi nasa mulkin a Sabongari /Sabongarin Damri ( a cikin Masarautar Bakura, Jihar Zamfara) sanadiyar matsin lambar da Gobirawa suka nunawa Zamfarawa bayan sun karɓe Birnin Zamfara daga gare su a lokacin mulkin Sarkin Gobir Ibrahim Babari ɗan Ashi/Ashe a cikin 1764, Daular Zamfara ta fuskanci mawuyacin hali, musamman samun hedikwata ta dindindin.
A lokacin mulkin Sarkin Zamfara Ɗanbaƙo ɗan Abarshi (1815-1824) ne ya dawo da hedikwatar Daular Zamfara a wannan ginannen gari na Anka. Kamar yadda aka ambata a sama Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ne ya ƙirƙiri Anka a matsayin mazauninsa.
Akwai ruwaya guda biyu game da tasowar Zamfarawa daga Sabongari /Sabongarin Damri zuwa Anka. Ta farko tana nuni da cewa ishara ce daga Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi da ta yiwa Zamfarawa izni a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Zamfara Ɗanbaƙo dake zaune a Sabongari/Sabongarin Damri da su yaƙi Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau dake garin Anka, su kore shi daga garin saboda su kwashe kayansu zuwa can (Anka) a matsayin sabuwar hedikwatarsu.
Ruwaya ta biyu kuma ta bayyana cewa Zamfarawan sun yi wa Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau sammu a kaɓakin tuwo inda suka aika wani mutum da ake kira Garangamau da kaɓakin tuwo daga Sabongari /Sabongarin Damri zuwa Anka wanda aka ce sanadiyar arba da sammun da Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya yi ne sai ya fice daga Birnin shi da jama'arsa bayan ya ƙona wasu sassan sa. A cewar wannan ruyawar, bayan fitar sa ne Sarkin Zamfara Ɗanbaƙo da jama'arsa suka kwaso kaya suka dawo Anka inda ya ci gaba da mulki har zuwa 1824 lokacin da suka cire shi suka kai shi gudun hijira a wani gari mai suna Bardi a cikin masarautar Bakura, Jihar Zamfara (babu wannan gari a halin yanzu).
Daga lokacin ne hedikwatar Daular Zamfara ta ci gaba da zama a garin Anka zuwa yau.
A waɗannan hotuna guda uku☝️☝️☝️ ana iya ganin Mai martaba Sarkin Zamfara Anka, Shugaban Majalisar Masarautun Jihar Zamfara, Alh. Muhammad Attahiru Ahmad CON da tsohon gidan sarauta na Anka wanda Malam Banaga Ɗanbature Ɗandanau ya gina da kuma yadda gwamnati mai ci yanzu ta Jihar Zamfara ta sabunta wannan gida.
Allah SWT ya jaddadawa magabatanmu rahama ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sayyadir Rahama Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.
Ana iya duba :- K. Krieger, Geschicte Von ZAMFARA, Berlin, 1959 da Garba Nadama, The Rise and Collapse of a Hausa State : A Social and Political History of Zamfara(Unpublished PhD Thesis), History Department, Ahmadu Bello University, Zaria, 1977 da kuma Dr. Sanusi Shehu Gusau, Rise and Expansion of Zamfara Kingdom : Birnin Zamfara to Anka, Conference Proceedings : Zamfara and the Challenges of Socio- Political Transformation From 1764-2019 Published by the Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, 2020 domin ƙarin bayani.
Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Jihar Zamfara, Nijeriya.
28/02/2026.