Ƙasar China ta yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na sauya gwamnati a Iran, tana mai cewa irin wannan mataki ba zai samu goyon bayan jama’ar Iran ba.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Beijing. Ya ce duk wani yunƙuri na tilasta sauyin gwamnati ko juyin mulki a Iran ba zai samu karɓuwa daga al’ummar ƙasar ba.
Wang Yi ya kuma yi kira da a dakatar da hare-haren soja nan take a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai roƙon dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin su koma kan teburin tattaunawa domin nemo mafita ta lumana.
Ya jaddada cewa dole ne a girmama ikon ƙasa da cikakken ‘yancin Iran, yana mai gargadin cewa duniya ba za ta koma tsarin da ƙasashe masu ƙarfi ke tilasta ra’ayinsu da ƙarfin soja ba.
China ta kuma bukaci manyan ƙasashen duniya su taka rawar gani wajen rage tashin hankali, tana mai cewa matsalolin yankin ya kamata a warware su ta tattaunawa da hanyoyin siyasa, ba ta hanyar yaƙi ba.