Isra’ila Ta Kai Hari Kan Cibiyoyin Man Fetur Na Iran A Karo Na Farko Yayin Da Yakin Ya Shiga Rana Ta Tara

 Sojojin Israel sun kai hare-haren sama kan cibiyoyin ajiyar man fetur a Iran, a karo na farko tun bayan fara yaƙin tsakanin ƙasashen biyu. Hare-haren sun auku ne a birnin Tehran da wasu yankuna kusa da shi yayin da yaƙin ya shiga rana ta tara. 

birnin Tehran

Rahotanni sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari kan wuraren ajiyar mai da cibiyoyin rarraba man fetur da ake zargin suna taimaka wa rundunonin sojan Iran. Harin ya janyo gobara mai ƙarfi da hayaƙi mai yawa da aka gani daga sassan birnin. 

A cewar kafafen yada labarai na Iran, aƙalla direbobin tankar mai huɗu sun mutu sakamakon hare-haren. Hukumomi sun ce jami’an kashe gobara sun yi ta kokarin shawo kan gobarar da ta tashi a wuraren ajiyar mai. 

Sojojin Isra’ila sun ce an kai harin ne kan cibiyoyin mai da ke bai wa sojojin Iran da sauran bangarorin tsaro man fetur, a wani mataki da Isra’ila ta ce yana cikin kokarinta na rage karfin sojan Iran. 

Harin ya zo ne yayin da rikicin tsakanin Israel da Iran ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, inda hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama ke ci gaba tsakanin bangarorin biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post