Desmond Elliot Ya Ki Amincewa da Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani na APC a Surulere I

Dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazabar Surulere I, Desmond Elliot, ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa zai ƙalubalanci tsarin zaɓen ta hanyar amfani da tsarin ɗaukaka ƙara na jam’iyyar.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Elliot ya rasa tikitin jam’iyyar APC na sake tsayawa takara a kujerar majalisar dokokin jihar Legas bayan da Barakat Odunuga-Bakare ta doke shi a zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar Laraba.

Odunuga-Bakare, wadda ake ganin tana da goyon bayan shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ta samu ƙuri’u 11,385 inda ta zama wadda ta lashe zaɓen, yayin da Elliot ya samu ƙuri’u 270 kacal.

Da yake zantawa da manema labarai bayan bayyana sakamakon, Elliot ya ce bai gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen ba, kuma zai shigar da ƙorafi a hukumance domin kalubalantar tsarin.

Ya ce:

“Muna ɗaukaka ƙara, kuma kamar yadda na faɗa, wannan ba batun sai an yi ko ba a yi ba ne. Ina nan ne domin yi wa jama’a hidima. Nan ne gidana, kuma mutane suna zuwa gidana.

“Ba zan ƙara cewa komai ba face dai ba mu amince da wannan tsarin ba. Amma jam’iyyar ta kuma ba mu damar ɗaukaka ƙara cikin adalci.”

Elliot ya kuma yi zargin cewa an samu tashin hankali da tsoratarwa yayin gudanar da zaɓen, yana mai cewa wasu daga cikin magoya bayansa sun samu raunuka a lokacin zaɓen fidda gwanin.

Post a Comment

Previous Post Next Post