Jam'iyar adawa ta PDP ta tsayar da malamin addinin Musulunci kuma tsohon minista a zamanin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, wato, Farfesa Ali Isah Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Gombe.
A baya bayan nan, an kai ruwa rana a jam'iyar APC, musamman akan abin da ya shafi sasanci (consensus) da aka tafka na neman takarar Gwamnan jihar Gombe, inda Gwamna mai ci ya yi tsayuwar gwanin jaki, tare da tabbatar da ya kwarfe Farfesa Ali Isah Pantami daga tsayawa takarar gwamnan jihar a jam'iyyar APC.
Bayan nan an yi ta yaɗa jita-jitar cewa, Pantami na shirin sauya sheƙa daga APC zuwa jam'iyyar adawa wato PDP. Wanda da yawan masu sharhi, suke ganin Pantami ba zai iya yin haka ba, saboda akwai barazanar za a iya tura jami'an farin kaya ko ICPC ko EFCC su kama shi kamar dai yadda aka yi wa tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i.
Kwatsam! Yau kuma sai ga shi mun tashi da labarin cewa. Jam'iyyar PDP ta tabbatar da Farfesa Ali Isah Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Gombe.