Ku zama cikin shiri; Sojoji sun yi gargadi ga yan arewa kan yiwuwar kai hare-hare a lokacin bikin sallah.
Rundunar sojin Najeriya ta gargaɗi mazauna yankin Arewa maso Gabashin ƙasar kan yiwuwar hare-haren ƙunar baƙin wake da na bama-bamai da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP za su iya kaiwa yayin bukukuwan Babbar Sallah.
A cikin wata sanarwa da shalkwatar rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce sahihan bayanan sirri sun nuna akwai yiwuwar mayaƙan ƙungiyoyin biyu za su yi amfani da lokacin bukukuwan Babbar Sallah wajen kai hare-hare kan fararen hula, musamman a wuraren da jama’a ke taruwa don gudanar da shagulgula.
Sanarwar ta ƙara da cewa, rundunar ta tura dakarunta zuwa muhimman wurare masu hadari a dukkanin sassan yankin, yayin da aka sanya na’urorin tattara bayanan sirri domin bibiyar duk wata barazana da kuma tallafa wa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.
Haka kuma sanarwar ta ce an ƙara yawan sintiri, tare da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da sauran hukumomi da kuma jami’an tsaro na JTF da ƙungiyoyin sa-kai, domin hana duk wata ɓaraka ta tsaro a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.
Haka kuma rundunar ta shawarci mazauna yankin su kasance cikin shiri tare da kauce wa zirga-zirgar da ba ta zama dole ba, musamman da daddare da kuma wuraren da babu jami’an tsaro.
Sanarwar ta kuma buƙaci jama’a su gudanar da sallar Idi da sauran bukukuwa a kusa da gidajensu, su guji manyan taruka, sannan su gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani mutum ko motsi da ba su gamsu da shi ba, ko kuma wani abu da aka yasar babu mai kula da shi.
Rundunar sojin ta kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa dakarunta na cikin shirin ko-ta-kwana, tare da cikakken shiri domin hana mayaƙan samun damar kai hare-hare a duk lokacin bukukuwan Sallah.
Rundunar ta ce ta jibge dakarunta tare da kayan sa ido domin daƙile duk wata barazana.
