Kamfanin Google ya daɗe yana sauya tsarin yadda injin bincikensa ke bayar da sakamako, inda yake ƙara nisanta kansa daga tsohon tsarin nuna jerin hanyoyin shiga yanar gizo kawai (“blue links”) zuwa tsarin da ke amfani da basirar wucin gadi (AI). Sai dai sabon fasalin injin binciken nasa, wanda ke aiki da sabon tsarin Gemini 3.5 Flash, ana ganin shi ne babban sauyin da kamfanin ya taɓa yi wajen mayar da hankali kan AI maimakon tsarin bincike na gargajiya.
A sabon tsarin, filin da ake rubuta bincike zai fi faɗi domin bai wa masu amfani damar yin dogayen tambayoyi cikin salon hira, irin yadda mutane ke tattaunawa da Gemini ko OpenAI’s ChatGPT.
Haka kuma, masu amfani za su iya ƙirƙirar abin da Google ya kira “agents” a cikin injin binciken, waɗanda za su iya bibiyar bayanai ko gudanar da bincike kan wasu batutuwa kai tsaye ba tare da sa hannun mai amfani a kowane lokaci ba.
Kamfanin ya bayyana cewa wannan sabon fasali zai taimaka musamman wajen ayyukan da ke buƙatar sa ido na dogon lokaci, kamar neman gidan haya ko bibiyar sabbin kayan sawa da ake fitarwa kasuwa.
Misali, mutum zai iya rubuta tambaya kamar:
“Ka ci gaba da sanar da ni duk lokacin da fitattun ‘yan wasan da nake bi suka sanar da haɗin gwiwar takalma ko sababbin nau’ikan takalmansu.”
Da zarar an bayar da wannan umarni, Google zai riƙa sa ido kan sanarwar da ‘yan wasa da manyan kamfanoni ke fitarwa tare da isar da sabbin bayanai ga mai amfani.
Bugu da ƙari, Google zai fara samar da zane-zane na musamman da ƙananan manhajoji kai tsaye bisa ga bukatar mai amfani. Misali, injin binciken zai iya ƙirƙirar manhajar bibiyar motsa jiki da za ta haɗa bayanan wurin da mutum yake, yanayin hasashen iska, da kuma wasu manhajojin da ke haɗe da asusun Google ɗinsa.