Hoton Da Aka Hana Yadawa A Thailand

An haramta yada wannan hotunan a Thailand, idan ka kuskura ka wallafa wadannan hotunan a cikin kasar, za a iya daure ka tsawon shekaru 10 a gidan yari.

Sarkin Thailand

Duk da cewa mutumin da ke cikin hoton ya yi kama da mai maye, amma shi ne, Sarkin Thailand, Phrabat Somdet Phra Poramenthra Ramathibodi Sisinthara Maha Vajiralongkorn Phra Wachiraklao Chao Yu Hua Vajiralongkorn Boromchakrayadisorn Santatiwong Thewetthamrongsuboribal Abhikktalmadungunukornade Kittisirisombunsawangwat Boromkhattiyarajakumarn. (sunansa kenan), yayin da yake shiga mota aka dauki hotonsa a cikin shekarar 2016.

An san wannan sarki da munanan dabi'u, kamar shan barasa da caca. Wannan hoton yana daya daga cikin hotunan da aka fi sanya ido ga duk wanda ya wallafa, saboda kyawawan dalilai, idan jama'a suka ga sarkinsu yana tambele to tabbas hakan zai haifar da hayaniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post