Jami’an Tsaro na Fuskantar Bincike Bayan Harbe-Harbe a Majalisar Dattawan Philippines

 Hukumomin Philippines sun fara bincike kan wasu jami’an tsaro na Majalisar Dattawa bayan harbe-harbe da suka faru a harabar majalisar a makon da ya gabata, lamarin da ya haifar da firgici da rudani a ƙasar. 

Philippines

Rahotanni sun bayyana cewa harbe-harben sun faru ne yayin da Sanata Ronald dela Rosa, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ke nema ruwa a jallo, ya nemi mafaka a cikin ginin Majalisar Dattawa domin kauce wa yiwuwar kama shi. 

Ministan harkokin cikin gida na Philippines, Juanito Victor Remulla, ya bayyana cewa shugaban jami’an tsaro na majalisar, Mao Aplasca, shi ne mutum na farko da ya fara harbi. Ya ce bayan wannan harbi ne wani jami’in gwamnati ya mayar da martani da harbin gargadi. 

Jami’ai sun ce dukkan alamu sun nuna cewa babu wani hari kai tsaye da aka kai kan Majalisar Dattawan, kuma jami’an gwamnati ba su shiga cikin ginin majalisar ba. Sai dai ana binciken ko jami’an tsaron sun yi amfani da makamansu ba tare da wani dalili na gaggawa ba. 

Binciken ya kuma mayar da hankali kan hotunan CCTV da kuma yadda Sanata dela Rosa ya samu damar ficewa daga majalisar cikin rikicin da ya biyo bayan harbe-harben. 

Lamarin ya sake ƙara zafafa rikicin siyasa a Philippines, musamman dangane da binciken ICC kan yaƙin da tsohon shugaban ƙasar Rodrigo Duterte ya yi da miyagun ƙwayoyi, wanda ake zargin ya yi sanadin kashe mutane da dama ba tare da shari’a ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post