Desmond Elliot Ya Bayyana Dalilin da ya Sa ya Sanya Hannu a Tsige Obasa

Dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazabar Surulere I, Desmond Elliot, ya bayyana yadda ya shiga cikin shirin tsige kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, a watan Janairun 2025, tare da bayyana dalilin da ya sa ya sanya hannu a takardar tsige shi.

Elliot ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da ya yi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels Television a ranar Talata.

Tsohon jarumin fina-finan wanda ya koma harkar siyasa ya ce yana mayar da martani ne kan kalaman shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya ce Elliot ya kusa rasa kujerarsa saboda rahotannin sirri da suka danganta shi da yunkurin tsige Obasa.

A cewar Elliot, a lokacin da lamarin ya faru ba ya cikin Najeriya, domin shi da matarsa sun yi tafiya a ranar 13 ga Janairun 2025 domin halartar bikin auren kanwar matarsa.

“Mun kasance cikin hutun majalisa, kuma hakan ya ba mu damar yin tafiya domin halartar bikin auren kanwar matata,” in ji shi.

Ya kara da cewa an tsige Obasa ne yayin da yake kasar South Africa, lamarin da ya zo masa da mamaki.

“A lokacin ne aka tsige Rt. Hon. Mudashiru Ajayi Obasa daga matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Legas.

“Hakan ya zo min da mamaki saboda ina kasar Afirka ta Kudu a lokacin. Sai da ya dauki kusan kwanaki biyu kafin in dawo gida. Ni ma na rude kamar yadda kowa ya rude,” in ji shi.

Elliot ya ce bayan dawowarsa ya tarar cewa kusan dukkan ‘yan majalisar sun riga sun sanya hannu a takardar tsige kakakin majalisar, kuma su na zaton matakin ya samu goyon bayan fadar shugaban kasa.

“Sannan na ga kusan kowa ya sanya hannu. Gaskiya mun yi zaton cewa daga fadar shugaban kasa aka ba da umarnin.

“Saboda haka ni ma na sanya hannu. Ina ganin ni ne mutum na talatin da wani abu da ya sanya hannu a lokacin,” in ji shi.

Ya ce daga bisani Shugaban kasa Bola Tinubu ya kira ‘yan majalisar tare da bayyana musu cewa ba shi ne ya bayar da umarnin tsige Obasa ba, sannan ya bukace su da su mayar da shi kan kujerarsa.

“Daga baya Shugaban kasa ya kira mu ya kuma bayyana mana cewa ba daga gare shi lamarin ya fito ba, sannan ya bukace mu da mu dawo da kakakin majalisar.

“Kuma haka muka yi,” in ji Elliot.

Da yake martani kan kalaman Gbajabiamila cewa ya kusa rasa kujerarsa, Elliot ya ce kalaman sun ba shi mamaki duba da dadadden alakarsu.

“Jagorana ya fito ya ce haka, alhali na dade ina aiki tare da shi kuma shi ma ya dade yana taimaka min. Don haka jin wannan magana daga gare shi ya ba ni mamaki,” in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post