ICPC ta Musanta Zargin Hana Matar El-Rufai Kai Masa Abinci a Tsare

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta musanta zargin da matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ta yi cewa an hana ta kai wa mijinta abinci yayin da yake tsare a hannun hukumar, tana mai jaddada cewa dokokin tsaro da tsarin shiga harabarta suna aiki ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Hukumar ta kuma ƙaryata ikirarin cewa lafiyar tsohon gwamnan na ci gaba da tabarbarewa, tana mai cewa El-Rufai yana cikin ƙoshin lafiya tare da samun abinci, kulawar lafiya da kuma ziyartar iyalansa bisa ƙa’idojin da aka tanada.

Da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ICPC da ke Abuja, kakakin hukumar kuma shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, John Odey, ya bayyana cewa zarge-zargen da ke yawo a cikin wani bidiyo da ɗaya daga cikin matan El-Rufai ta yi “ƙarya ne kuma masu yaudara.”

Ya bayyana cewa tsarin kula da shiga harabar hukumar yana bai wa baƙi damar shiga ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa 6:30 na yamma, yana mai cewa wannan tsari ya daɗe kafin shugabancin hukumar na yanzu kuma ana aiwatar da shi a dukkan ofisoshin hukumar a faɗin ƙasa.

A cewarsa, matar da ake magana a kanta ta isa harabar hukumar ne da misalin ƙarfe 7 na yamma, bayan lokacin da aka amince da shiga, duk da cewa a baya ta kasance tana bin ƙa’idar.

“ICPC na son bayyana karara cewa waɗannan zarge-zarge ƙarya ne kuma masu yaudara,” in ji shi.

Odey ya ƙara da cewa an bai wa ‘yan uwan El-Rufai damar kai masa abinci sau da dama a wannan rana.

“A ranar Juma’ar da ake magana a kai, ɗaya daga cikin matan wanda ake tsare da kuma wata mai aikin gida sun samu damar kawo masa abinci ba ƙasa da sau uku ba, tsakanin ƙarfe 10:30 na safe zuwa 5:30 na yamma,” in ji Odey.

Yayin da yake nuna wasu sassan rajistar baƙi da ke tabbatar da yawan shigar ‘yan uwan El-Rufai cikin harabar hukumar, Odey ya ce, “Akwai shigar sunaye guda shida na ‘yan wannan iyali da suka zo nan domin kawo masa karin kumallo, abincin rana da na dare yayin da yake tsare a hannunmu.”

Post a Comment

Previous Post Next Post