Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Fara Yunƙurin Ƙarin Albashi Duk da Matsalolin Aiwatar da ₦70,000 a Jihohi

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun fara matsa lamba domin sake duba mafi ƙarancin albashi na ƙasa, duk da koke-koken da ake yi cewa har yanzu wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da albashin ₦70,000 da aka amince da shi tun shekarar 2024 ba.

Lamarin na ƙara janyo saɓani tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatocin jihohi, inda ƙungiyoyi kamar Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi (NULGE), da Ƙungiyar Malaman Makarantu (NUT) ke zargin wasu gwamnoni da aiwatar da dokar albashin ne kawai ga wasu ma’aikata.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 a ranar 29 ga Yulin 2024, inda aka ƙara shi daga ₦30,000.

Sai dai kusan shekaru biyu bayan haka, shugabannin ƙwadago sun ce aiwatar da dokar bai daidaita a faɗin ƙasar nan ba, musamman ga ma’aikatan ƙananan hukumomi, malaman firamare, da ma’aikatan cibiyoyin lafiya na matakin farko.

Jihohin da aka fi ambata a cikin koke-koken ƙwadago sun haɗa da Yobe, Zamfara, Gombe, Kaduna, Imo, Ebonyi, Cross River, Borno, Sokoto, Taraba, Bauchi, Nasarawa, Adamawa, Abia, Benue, Niger, Kogi da kuma ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ƙungiyoyin sun yi zargin cewa duk da wasu gwamnoni sun bayyana a bainar jama’a cewa sun fara biyan sabon albashin, dubban ma’aikata har yanzu suna karɓar tsohon albashi, yayin da batun ƙarin alawus-alawus da bashin kuɗaɗen baya bai warware ba.

Saboda ƙara tsanantar takaicin ma’aikata, NLC ta umarci rassanta da ke jihohin da ba su aiwatar da dokar ba su kaurace wa bukukuwan Ranar Ma’aikata ta shekarar 2026, maimakon haka su gudanar da zanga-zangar lumana a tituna.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce:

“Ku gudanar da bikin ranar Ma’aikata ta 2026 a kan tituna idan har ba a aiwatar da Dokar Mafi Ƙarancin Albashi gaba ɗaya a jiharku ba.”

NLC ta kuma gargaɗi mambobinta da kada su gudanar da bukukuwan Ranar Ma’aikata a cikin harabar gidan gwamnati ko wuraren da aka shirya tare da gwamnatocin jihohin da ake zargi da rashin aiwatar da dokar albashin.

Post a Comment

Previous Post Next Post