Hukumar Kula da Yi wa Ƙasa Hidima ta Ƙasa wato National Youth Service Corps ta sanar da cewa daga zangon horaswa na 2026 Batch ‘B’ Stream 1, duk masu shirin shiga yi wa ƙasa hidima za su kasance wajibi su gabatar da takardar shaidar bin ƙa’ida daga cibiyar adana bayanan ilimi ta ƙasa, wato Nigeria Education Repository and Databank, a matsayin wani ɓangare na tsarin tantancewa kafin a tura su bautar ƙasa.
Babban Daraktan hukumar ta NYSC, Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin taron shirin tantance masu shiga hidimar ƙasa na 2026 Batch ‘B’, mai taken “Strengthening Institutional Accountability and Compliance in the NYSC Mobilization Process.”Nafiu ya ce sabon matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana, daƙile amfani da takardun bogi, tare da tabbatar da cewa ƙwararrun waɗanda suka cancanta ne kaɗai ake tura wa bautar ƙasa.
Ya ce, “A ƙoƙarinmu na ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana, ina sanar da cewa daga zangon horaswa na 2026 Batch ‘B’ Stream 1, hukumar NYSC za ta fara aiwatar da umarnin Federal Executive Council wanda ya wajabta wa duk masu shirin shiga bautar ƙasa samun da kuma gabatar da takardar shaidar bin ƙa’ida daga NERD.”
Ya ƙara da cewa wannan tsari wani muhimmin mataki ne na dakile damfarar takardun shaida tare da tabbatar da cewa waɗanda suka kammala karatu na gaskiya ne kaɗai ake tantancewa domin yi wa ƙasa hidima.
Shugaban NYSC ɗin ya bayyana cewa wannan sauyi ya yi daidai da umarnin Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin tsaftace tsarin tattara bayanan masu bautar ƙasa da kuma dawo da martabar tsarin.
Nafiu ya jaddada cewa tsarin tantance masu bautar ƙasa ba aikin NYSC kaɗai ba ne, illa haɗin gwiwa ne tsakanin NYSC, cibiyoyin da suka yaye ɗalibai, Joint Admissions and Matriculation Board da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki.
Ya ce, “Tsarin tattara bayanan masu bautar ƙasa aiki ne na bai ɗaya. Idan muka yi aiki tare cikin haɗin kai, za mu sauƙaƙa wa masu shirin bautar ƙasa hanyarsu daga rayuwar ɗalibanci zuwa bautar ƙasa cikin gaskiya da sahihanci.”
Haka kuma ya buƙaci cibiyoyin ilimi su tabbatar da bin ƙa’idojin tattara bayanan ɗalibai yadda ya kamata, tare da yin gargaɗi kan sauya ko karkatar da bayanan waɗanda aka tura domin bautar ƙasa.