Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Je Asibiti Duba Direban Tsohon Sojan Da Aka Yi Garkuwa Da Shi

Mai girma mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon. Garin Yawan Jobe ya ziyarci direban tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar da 'uan bindiga suka yi garkuwa da shi a kan hanyar matazu a shekara jiya. 

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, ya kai ziyarar jinya ga direban tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, bayan harin da 'yan bindiga suka kai masu a hanyar Matazu, wanda ya samu rauni ta hanyar harbin bindiga, da ɓarayin dajin suka yi masa, sai dai Allah ya taimake shi ya gudu ba su tafi da shi ba.

Mataimakin gwamnan ya kai ziyarar ne a asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina, inda ake kula da lafiyar matuƙin. 

A baya-baya mataimakin gwamnan ya shaidawa duniya cewa, babu hanyar da a bi a Katsina saboda tsabar samun sauƙin tsaro da aka yi, sai dai ko kwana biyu ba a yi da maganarsa ba, sai ga wannan aika-aikar an tafka a ƙaramar hukumar Matazu.

A yayin ziyarar, Malam Faruk Jobe ya jajanta wa wanda lamarin ya shafa tare da yi masa fatan samun cikakkiyar lafiya cikin gaggawa. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar Katsina na ci gaba da ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin ganin an ƙara inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Har wa yau, ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba wa hukumomin tsaro haɗin kai da sahihan bayanai waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Post a Comment

Previous Post Next Post