Peter Obi ya yi Allah-wadai da hare-haren da kuma sace ɗaliban makarantu da aka yi a wasu sassan jihohin Borno da Oyo, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin barazana mai ƙara ta’azzara ga tsarin ilimi da makomar ƙasar nan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Obi ya ce sace ɗalibai daga makarantu a ƙauyen Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno, da kuma al’ummar Ahoro-Esinele da ke ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, alama ce ta yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara muni a ƙasar.Ya ce, “Abin takaici ne yadda yanzu yara ‘yan makaranta suka zama tamkar kayan ciniki a tattalin arzikin kuɗin fansa. Babu abin da ya fi karya zuciyar ƙasa kamar gazawar kare yaranta.”
Obi ya gargaɗi cewa yawaitar kai hare-hare kan makarantu ba wai gazawar tsaro kaɗai ba ce, har ila yau hari ne kai tsaye kan haƙƙin yara na samun ilimi. Ya ƙara da cewa tsoron sace yara yana tilasta wa ɗalibai da dama, musamman ‘yan mata, barin makaranta.
A cewarsa, “Hare-haren baya-bayan nan da aka kai tare da sace ɗalibai daga makarantu biyu — a ƙauyen Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno a Arewa maso Gabas, da kuma al’ummar Ahoro-Esinele da ke ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo a Kudu maso Yamma — sun nuna wata babbar matsala da ke barazana ga makomar ƙasar nan.”
Ya kuma yi gargaɗin cewa tsoron sace yara yana rage sha’awar zuwa makaranta, musamman ga ‘yan mata, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.