Sarki Aliyu Yaji Dan Tsamiya yana daya daga cikin Sarakunan Kano. Yaji I ya yi mulki daga shekara ta 1359 zuwa 1385 (Yau sama da shekaru 700 miladiyya). Sarki Yaji Wani fitaccen jigo ne a tarihi. Yaji shi ne ya yi juyin juya hali na addini, kuma shi ne sarkin da ya ci Rano ya shigar da ita cikin Kano da karfi da Yaji (kamar yadda kalmar da karfi da Yaji ta samo asali a harshen Hausa).
Sarki Yaji ya gaji Sarauta daga mahaifinsa Sarkin Kano Tsamiya, sunan mahaifiyarsa Maganarku.
Sarki Yaji shi ne sarki na goma sha ɗaya a jerin sarakunan Kano. Asalin sunansa Ali, saboda zafin zuciya da yake da ita shi ya saka ake kiransa da sarki Yaji. Shi ne ya kori sarkin Rano daga Zamnagaba. Ya zauna a Bono tsawon shekaru biyu. Sannan ya tafi Kura ya zauna tare da Ajawa, Warjawa da Arawa.
A lokacinsa ne Wangarawa daga mali suka zo Kano suka Kawo Musulunci. Sarki Yaji ya karɓi wangarawa hannu biyu-biyu, a hannunsu ya karɓi salla karkashin jagorancin Abdulrahman Zaite. Tarihi ya lissafo sunayen wasu malaman kamar su Yakubu, Mandawari, Famori, Bilkasirn, Kanaji, Dukere, Sheshe, Kebe, Murtuku, Liman Jibrin Yallabu, mahaifin Sarkin Pawa, Gurdumlius, Auta, Laual, da Liman Madatai.
Sannan ya gina musu masallaci a gurbin da ya karya gunkin Tsimbirbira (A Yankin Dala kenan). Kuma shi ne sarkin Kano na farko da ya gina masallacin juma'a na farko a Kano a unguwar juma ta cikin garin kano (ta samo asalin sunanta ne daga masallacin juma'a da aka gina a unguwar). Sarki Yaji shi ne ya shelanta Kano a matsayin masarautar Sarkin Musulmi.
Yaji ya nada malam Zaite Alkali (Qadi), da Laual a matsayin ladani, da Gurdamus a matsayin Liman (Imaminsa). An kuma nada Auta malamin yanka dabbobi. Daga nan sai Yaji ya umurci talakawansa a duk garuruwan Kano da su kiyaye salloli biyar da aka wajabta. Ya kuma gina wani masallaci da ke fuskantar Ka'aba a karkashin wata bishiya a Kano.
.Sarkin Gazarzawa Yaki musulunta
Sarkin Gazarzawa wanda ɗaya ne daga cikin maguzawan da sukai saura, yakan ɗebi jama’arsa kullum da dare su je su yi najasa (kashi) sannan su gogga a jikin masallacin. Ganin haka ta saka sarki ya saka mai gadi amma basu daina ba. Sukan je su yaudare shi. Basu daina wannan mummunan aiki ba har sai da Wangarawa suka yi addu’a Allah ya makantar da su. Bayan makancewarsa aka tuɓe shi daga sarauta (sarkin Gazarzawa) sannan aka yi masa sarkin makafi (sune asalin makafin Dala). Wannan ita ce farkon sarautar makafi a Kano.
Haka nan sarki ya umarci dukkan jama’ar masarautarsa da salla kuma suka bi. Bayan wannan sarki Yaji shi ya ci Santolo da yaki. Ya roki malaman Wangarwa da su masa addu’a ya je ya yaki Santolo. A wannan lokacin, Santolo ita ce kaɗai babbar kasa da ta rage. Kuma cin ta da yaki zai karya lagon duk wani mai bautar gunki. Hakan kuwa aka yi, jama’ar Wangarwa da Kanawa suka haɗu suka tada runduna mai karfi suka ɗunguma zuwa Santolo. A rana ta farko an wuni ana gwabzawa amma ba wanda ya yi galaba a kan wani. Kashegari da fudowar alfijir sarki ya ɗaura ɗamarar yaki. Suna shiga a wannan rana Allah ya kawo musu nasara.
Sarki Yaji ya yi sauratar Kano na tsawon shekaru talatin da bakwai. Hakika ya kawo ci gaba sosai a wannan masarauta ta Kano.
TASIRI
Ana ganin Yaji I a matsayin daya daga cikin manyan sarakuna da mayaka a tarihin Kano. Ana tunawa da shi a matsayin Sarkin Kano na farko wanda ya yi jihadin Musulunci na farko a yankin. Ayyukan Yaji sun taka muhimmiyar rawa yayin da suka share hanyar da Kano ta samu na daukaka a tsakanin kasashen Hausa da Afrika ta Sudan.
KIRARIN YAJI
"Yaji maci tudu, mai warwatsa runduna, Ubangijin gari"
IYALI
Yaji yana da, da' Kanajeji tare da Aunaka. Kanajeji ya zama sarkin Kano na 13.
