"Yakin Zaɓen Tinubu 2023 Shi Ne Mafi Munin Abu A Rayuwata." Fati Karishma

A fitar da Hadiza Gabon ta yi da fitacciyar 'yar wasan Hausar nan (Kannywood) Fati Karishma a filinta na Gabon Talkshow. Fati ya bayyana cewa: Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai ci Bila Ahmad Tinubu da aka yi a shekarar 2023 shi ne Abu mafi muni a rayuwarta. Ta bayyana haka ne sakamakon a lokacin yawon neman zaɓen ne ta haɗu da wani babban mutum, wanda ba ta ambaci sunansa ba a firar, wanda suka fara soyayya har ya kai su ga aure.

Sai dai sun kwashe shekara guda cur ba tare da ya zo inda take ko ta je inda yake ba.

Fati ta bayyana cewa: Da farkon auren ya kama min gida Mai tsada a Abuja kuma yana ba ni kulawa ta hanyar yi min duk abin da nake so duk da kasancewar ba ma tare da shi, domin shi ya kama min gida ya ba ni kuɗi na sayi dukkan kayan da ke cikin gidan na alatu, kuma yana tura min da kuɗib cefane a kai, a kai. Sai dai kwatsam bayan wasu 'yan watanni labari sai ya fara canzawa.

"Ya daina tura min da kuɗin cefane, tun yana amsa wayata har ya kai ga ya daina amsa kirana. A daidai lokacin kuma wasu cututtuka suka haura min, haka nan sai in yi ta zubar da jini, aƙalla ina zubar da jinin da ya kai yawan penta (ƙaramar romar fenti), na je asibiti an yi aune-aune amma likitoci sun kasa gano mene ne matsalar."

Hankici ta sa ta share hawayen da ke Daman rigyangyato a saman kuncinta, sannan ya ci gaba.

"Ina cikin fama da wannan ciwo, sai kuɗin haya na ya ƙare, ana son in sake biya, amma abu ya ci tura, domin dukkan kayan ɗakina na riga na kaɗar da su, domin kula da kaina da abinci da kuɗin makarantar 'ya'yana guda biyu da nike tare da su. A haka na je wurin aikinsa da yake a Villa yake aiki, bayan na je aka tare ni a bakin gare, aka tambaye ni wurin wa na zo, na faɗa masu, ƙarshe dai ba su bar ni na shiga ba, sai da na kira masu shi a waya, a haka ya ce min in koma gida zai zo ya sake ni. Shiru-shiru bai zo ba, har na sake komawa wurin aikinsa, amma wannan karon sai na canza ƙofa, a nan kuwa na yi sa'a na gamu da masu gadin gidansa, sai dai duk da haƙa ta ba ta cin ma ruwa ba, domin nan ma wayar aka yi, ya nuna shi sam bai san ni ba, ballantana ya san wata maganar aure. Su kuwa masu haya da suka ga abin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai kawai suka kai ni kotu, ƙarshe dai na rabu da gidan na koma Jos mahaifata gidan iyayena, nan ma dai abin bai yi min daɗi ba domin na koma tamkar jaɓa ko mujiya babu wanda yake son in raɓe shi. Duk wanda na je wurinsa kyarata yake ba ya saon taimakona kamar wanda bai sanni ba, haka na ci gaba da zama har sai ta kai ga na yi ƙaura na koma Kano gidan wata ƙawata, wadda na yi mata dukkan abin da ake yi wa abokin a rayuwa, amma daga ƙarshe 'yan aiki muka zama ni da 'ya'yana a gidanta. Daga ƙarshe dai muka gudu muka koma gidan wata ƙawar tawa domin nema wa kai sauƙi."

"Babu babban abin tashin hankali, sai lokacin da na nemi mutumin nan ya sauwaƙe min, don ka da in yi ta yawo da aure kaina, tun da dai Ni musulma ce na san haƙƙin Allah da na aure da ya rataya a wuyana. Amma mutumin nan ya ƙeƙashe ƙasa, ya ce bai san ni ba, don haka, bai ga ta yadda zai saki abin da bai aura ba. Ƙarshe dai dole sai kotu na je aka raba auren, aka yi min saƙi ɗaya."

Ana cikin haka kuma, sai mahaifina ya kwanta ciwo, wanda ya kai ga hatta numfashi ba ya iya yi sai ta Oxygen, a lokacin da aka faɗa min rashin lafiyarsa ina Kano, kuma ba na maganin Naira 10, a nan ne fa Fantimoti da wata suka haɗa min kuɗin mota na tafi, ina jinyar mahaifina kuma ina jinyar kaina, da yawan 'yan Kannywood sun taimake ni sosai, domin Aminu Saira ya tura min 100k, Abba Elmustafa ya ba Ni 20k da sauransu. Amma Mansura Isah na kira ta domin neman agajinta, ta ce min za ta kira Rarara da Maishadda domin su taimake ni, amma har yanzu ɗin nan ba ta kira su kuma ba ta ƙara kirana ba, idan ma na kira ta ba ta ɗauka."

"In taƙaice maku zance har yanzu ɗin nan ba lafiya ce da ni ba, kuma har yanzu a gidan ƙawa nike zaune ni da 'ya'yana biyu." Fati Karishma 

Post a Comment

Previous Post Next Post