Majalisar Wakilai ta ƙasa ta amince a ranar Alhamis da kudirin dokar da Shugaban Ƙasa ya gabatar na kafa rundunar 'yan sandan jihohi, lamarin da ke nuna wani muhimmin mataki na sauya tsarin tsaron Najeriya ta hanyar bai wa jihohi damar mallakar nasu rundunar 'yan sanda.
An amince da kudirin ne a zaman majalisar bayan ta janye tsohon kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar kan kafa 'yan sandan jihohi, inda ta zaɓi rungumar kudirin da bangaren zartarwa ya gabatar, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Amincewar da Majalisar Wakilan ta yi ta biyo bayan sahalewar da Majalisar Dattawa ta ba wa nata sigar kudirin, abin da ya ƙara kusantar da Najeriya ga aiwatar da tsarin rundunonin 'yan sanda biyu, domin ƙarfafa tsaron cikin gida da inganta aikin tabbatar da doka da oda a matakin jihohi.