Shugaban ƙasar Yoweri Museveni na ƙasar Uganda, ya sake rantsar da kansa domin fara wa’adi na bakwai a matsayin shugaban ƙasa, lamarin da ya ƙara tsawaita mulkinsa zuwa kusan shekaru 40 yana kan karagar mulki. An gudanar da bikin rantsuwar ne a birnin Kampala a ranar Talata, inda manyan jami’an gwamnati da baƙi daga ƙasashe daban-daban suka halarta.
Museveni mai shekaru 81 a duniya, ya hau mulki tun shekarar 1986 bayan ya jagoranci yaƙin ƙwatar iko. Hukumar zaɓen Uganda ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu da fiye da kashi 71 cikin 100 na ƙuri’u. Sai dai ‘yan adawa sun yi zargin cewa an tafka magudi da kuma amfani da ƙarfi yayin gudanar da zaɓen.
A jawabinsa bayan rantsuwa, Museveni ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziki da rage talauci a ƙasar. Ya kuma bayyana cewa Uganda na shirin samun ci gaba mai yawa musamman da ake sa ran fara hako ɗanyen mai a ƙasar.
Sai dai ana ci gaba da samun muhawara kan makomar shugabancin Uganda, musamman saboda rade-radin cewa ɗansa, Janar Muhoozi Kainerugaba, wanda shi ne shugaban rundunar sojin ƙasar, na iya zama magajinsa a nan gaba.