Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Savannah Shield sun kama wasu mutane biyar da ake zargin masu ba ’yan bindiga da ’yan ta’adda bayanai ne a wasu samame daban-daban da suka gudanar a Jihar Neja.
Mukaddashin Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Jamilu Yahaya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce an gudanar da kamen ne yayin sintiri na yau da kullum a sassa daban-daban na jihar.
A cewarsa, a ranar 6 ga watan Yuni, 2026, dakaru sun kama mutane uku a yankin Doro da ke Wawa, Karamar Hukumar Borgu, wadanda ake zargin suna da alaka da wata kungiyar ’yan bindiga da ke aiki a kusa da dajin Kainji Lake National Park.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin na cikin wata kungiyar ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukanta a yankin Duru da kewaye.
Ya ƙara da cewa an kwato kayayyaki daga hannunsu da suka hada da wayoyin hannu guda biyu na Tecno masu madannai, na’urar MP3 da kuma kudi har Naira 113,400.
A halin yanzu, dukkan wadanda aka kama suna tsare domin ci gaba da bincike, yayin da dakarun ke ci gaba da kokarin gano sauran mutanen da ake zargin suna cikin wannan hanyar sadarwa.
