An Yi Taron Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A London.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Arsenal ta tara dubundubatar masoya wajen taya su murnar lashe gasar cin kofin Premier League da suka yi karo na 22 tun daga kafuwar ƙungiyar.
Bayanai na nuna cewa, ba a taɓa yin tarin cin murnar wata gasa ta cin wani kofi da ya tara yawan waɗannan mutanen a birnin London, duk kuwa da kasancewa ƙungiyar Chelsea ta taɓa lashe gasar kofin Zakarun Turai.
A yayin taron an soka wa mutane 6 wuƙa, sai dai abin ya zo da sauƙi, amma tuni aka garzaya da mutum ɗaya cikin waɗanda aka soka da wuƙar zuwa asibiti. Ya zuwa yanzu dai an kama mutane 24 waɗanda ake zargi suna da hannu a aika-aikar.
Wani rahoton na nuna cewa, an zuba 'yan sanda sama dubu biyar (5000) domin kula da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma.
An ƙiyasta aƙalla mutane sama da miliyan ɗaya da rabi 1.5m ne suka halarci tattakin murnar gasar cin kofin Premier League da ƙungiyar Arsenal ɗin ta lashe a London.
An gudanar da taron ne a jiya Lahadi bayan da ƙungiyar ta Arsenal ta sha kashi a hannu ƙungiyar PSG a wasan zagayen ƙarshe na cin kofin Zakarun Turai (Champions League).
Tags
Wasanni