Tsohon Janar Na Gwamnatin Bashar Al-Assad Ya Musanta Zargin Azabtarwa a Kotu

 Wani tsohon janar na gwamnatin tsohon shugaban Bashar al-Assad ta Syria ya musanta zarge-zargen azabtarwa da ake masa a wata shari’a da ake yi a ƙasar Austria.

Bashar al-Assad

Brigadier Janar Khaled al-Halabi ya gurfana a gaban kotu a birnin Vienna tare da tsohon jami’in ‘yan sanda Musab Abu Rukbah, inda dukansu suka musanta zarge-zargen da suka haɗa da azabtarwa, cin zarafi, tilastawa, da haddasa mummunan rauni ga mutane a lokacin yaƙin basasar Syria.

Masu gabatar da ƙara sun ce mutanen biyu suna da hannu wajen muzgunawa masu adawa da gwamnatin Assad a birnin Raqqa tsakanin shekarun 2011 zuwa 2013, a farkon shekarun rikicin Syria.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin waɗanda ake tuhuma da bayar da umarni, shiga kai tsaye, ko kuma gaza hana azabtarwa da cin zarafin waɗanda aka tsare saboda alaƙarsu da zanga-zangar adawa da gwamnati.

Idan aka same su da laifi, za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru har goma a gidan yari.

Shari’ar na daga cikin ƙalilan da ƙasashen Turai ke amfani da dokar “universal jurisdiction” wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan yaƙi da take haƙƙin ɗan adam da aka aikata a wajen ƙasarsu.

Khaled al-Halabi, wanda ke tsare a Austria tun shekarar 2024, ya ce bai taɓa shiga ko ganin azabtarwa ba, yana mai cewa ba shi da hannu a ayyukan cin zarafin da jami’an tsaron gwamnatin Assad suka aikata.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da masu fafutukar Syria sun bayyana cewa shari’ar wani muhimmin mataki ne wajen neman adalci kan laifukan yaƙi da take haƙƙin ɗan adam da aka aikata a lokacin rikicin Syria.

Post a Comment

Previous Post Next Post