Firaministan Hungary, Peter Magyar, ya sanar da shirinsa na yin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin cire shugaban ƙasa Tamas Sulyok daga muƙaminsa.
Magyar ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya gaza cika aikinsa yadda ya kamata, yana mai zargin sa da kasancewa kusa da tsohon firaminista Viktor Orbán da kuma kare tsarin mulkinsa.
Jam’iyyar Tisza ta Magyar ta samu rinjaye mai ƙarfi a zaɓen da aka gudanar a watan Afrilu, inda ta samu rinjayen kujeru fiye da kashi biyu cikin uku na majalisa, abin da ke ba ta damar yin sauye-sauye masu girma a kundin tsarin mulki.
Rahotanni sun nuna cewa Magyar ya bai wa Sulyok wa’adin yin murabus kafin ƙarshen makon da ya gabata, amma shugaban ya ƙi sauka daga mukaminsa. Firaministan ya ce idan shugaban bai yi murabus ba, gwamnati za ta fara amfani da hanyoyin doka domin cire shi daga mulki.
Ko da yake shugaban ƙasar Hungary na da galibin ayyuka na alama ne kawai, yana da ikon rattaba hannu kan dokoki da kuma mayar da wasu dokoki zuwa kotun tsarin mulki domin sake dubawa, lamarin da gwamnatin Magyar ke ganin zai iya hana aiwatar da sauye-sauyenta.
Jam’iyyar Fidesz ta tsohon shugaban gwamnati Viktor Orbán ta soki wannan yunkuri, tana mai cewa ƙoƙarin cire shugaban ƙasar na iya haifar da rikicin tsarin mulki da kuma lalata dimokuraɗiyyar ƙasar.
Magyar ya ce manufarsa ita ce sake gina tsarin dimokuraɗiyya da dawo da amincewar jama’a ga manyan hukumomin ƙasar bayan shekaru 16 na mulkin Orban.