Malam Muhammad Abubakar Bello Masaba, wani malami da ya rasu yana da shekaru 93 a duniya. Ya bar mata 130, yara 203. A cikin matan bakwai su na da ciki, da daya mai goyon ƙaramin yaro mai shekara ɗaya.
Muhammadu Bello Abubahkar Masaba Bida wanda aka haifa a watan Janairu 1924 kuma ya rasu a ranar 28 ga watan Junairun 2017, an fi saninsa da Muhammad Bello Abubakar, dan Najeriya ne, Masaba dai ya dauki hankalin jama'a ne a garinsu na Bida a jihar Neja saboda auren mata barkatai, sannan an tuhume shi da a kotun shari’ar Musulunci, kuma aka kai shi gidan yari a shekarar 2008 saboda ya ki sakin matan zuwa adadin da musulunci ya kayyade. Musulunci ya kayyade adadin matan da namiji musulmi zai iya aura zuwa hudu. Ya auri mata 130, ya saki 10, ya kuma haifi ‘ya’ya 203. A lokacin da ya rasu a shekarar 2017, an yi imanin wasu daga cikin matansa na da juna biyu.
Yayin da yake tsare wasu matansa da ‘ya’yansa sun gudanar da zanga-zanga. Daya daga cikin yaran da suka yi zanga-zangar a lokacin, Moroof Bello, ya bayyana mahaifinsu a matsayin mutum mai tsoron Allah.
Masaba malami ne kuma limami. Ya zauna a wani katafaren gida da iyalinsa. Masaba ya yi ikirarin cewa bai taba neman auren matan ba, yace su ne suka neme shi saboda matsayinsa na malami mai warkarwa. Yawancin matan nasa ba su kai shekaru 30 ba. A cikin hira da Al Jazeera English, matansa sun yi iƙirarin cewa shi miji ne nagari kuma uba.
A ranar 12 ga Nuwamba, 2008, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Maitama, Abuja, ta ba da umarnin a saki Masaba daga gidan yarin Minna ba tare da bata lokaci ba. Alkalin babbar kotun, Mai shari’a GO Kolawole, ya bayar da belin sakin sa. Alkalin ya kuma umarci Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mike Okiro da ya tabbatar da kare hakkin Masaba na rayuwa da walwala da kuma sirrinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada. Masaba ya koma garinsu, Bida, a ranar 13 ga Nuwamba, 2008.
A watan Yulin 2011, gwamnan jihar Neja Mu'azu Babangida Aliyu, ya ce "duk da cewa mun dabbaka tsarin Shari'a a jihar Neja, amma ba mu da wata doka da za ta hukunta shi. Yunkurin gwamnatin jihar Neja na gurfanar da Masaba bai yi nasara ba saboda rashin ayar doka. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Adamu Usman, ya bayyana cewa yunkurin da ake yi na gurfanar da Masaba a gaban kuliya ya ci karo da cikas, domin babu wani tanadi a dokar jihar da za ta iya hukunta shi.
