Shugaban ƙungiyar ’yan bindigar da ke riƙe da Manjo Janar Rabe mai ritaya da matarsa, Muhammadu Kachalla, ya bayyana dalilin da ya sa ya fasa shirinsa da ya yi na sakin matar tsohon jami’in sojan.
A cikin wani sautin murya da aka yaɗa, wanda ya ƙunshi tattaunawa tsakanin Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu da Kachalla Muhammadu Fulani, an ji shugaban ’yan bindigar yana cewa tun farko ya amince da sakin matar Janar ɗin, amma daga baya ya canja ra’ayinsa saboda yawan jami’an tsaro da aka tura yankin Matazu.
A cewarsa, da ya saki matar a irin wannan yanayi, da jami’an tsaro za su yi iƙirarin cewa su ne suka kuɓutar da ita.
“Na yi wa Janar alƙawarin zan saki matarsa, amma yawan jami’an tsaro da aka jibge a yankin ya sa na fasa. Da na sake ta, da sun ɗauke ta sun kai ta ofishin ’yan sanda na Matazu su ce su ne suka ceto ta,” in ji shi.
Ɗan ta’addan ya kuma nuna fushinsa kan kama wasu mutane da ya ce suna da alaƙa da ƙungiyarsa, yana mai cewa da iyayensa suna cikin waɗanda aka kama, da tuni ya kashe Janar Rabe.
“Ko sojoji 1,000 aka turo ba za su iya gano inda Janar yake ba. Da mahaifiyata ko mahaifina suna cikin waɗanda aka kama, wallahi da na kashe Janar yau, domin nuna wa gwamnati cewa ba za ta iya tsoratar da mu ba,” in ji shi.
Ɗan ta’addan ya kara da cewa idan har ana son tattaunawar sulhu ta kasance ta gaskiya, ya kamata a janye jami’an tsaron da aka tura yankin.
Ya kuma sake jaddada buƙatar a saki wasu mutum uku da gwamnati take tsare da su tare da mayar masa da dabbobin da ya ce an ƙwace a yayin ayyukan tsaro a yankin Jiƙamshi.
Ya kuma yi alƙawarin ficewa daga yankin tare da dakatar da hare-hare idan aka biya waɗannan buƙatu.
Har ila yau, ya yi zargin cewa ya mutunta yarjejeniyar sulhu da aka yi a baya, amma ya zargi jami’an gwamnati da karya alƙawarin da suka ɗauka.
Muna Da Ķwarin Gwiwar Ceto Janar Rabe Abubakar, Cewar Gwamnatin Katsina
A nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana ƙwarin gwiwar cewa ayyukan tsaro da ake gudanarwa za su kai ga ceto Janar Rabe da matarsa.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango, ya fitar ranar Asabar, ya ce haɗin gwiwar hukumomin tsaro da cibiyoyin tattara bayanan sirri ya kai wani mataki mai kyau.
Sanarwar ta ce nan da nan bayan faruwar lamarin, Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya umarci hukumomin tsaro da su ba da fifiko ga ƙoƙarin tabbatar da an ceto ma’auratan da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa.
Gwamnatin ta ce binciken farko ya nuna cewa hadafin masu garkuwar shi ne Janar Rabe da matarsa, inda ake zargin sun bi diddigin motsinsu tun daga Kaduna kafin kai harin.
Ta ce yanayin yadda aka aiwatar da harin na nuna hannun wata ƙungiya mai tsari, kuma hakan na nuni da sabon salo mai tayar da hankali da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke amfani da shi a yankin Arewa maso Yamma.
“Yadda aka aiwatar da wannan harin na nuna cewa aiki ne da aka shirya musamman domin kaiwa ga waɗannan mutane. Wannan ya sauya yadda muke kallon lamarin da kuma matakan mayar da martani. Gwamnati na aiki dare da rana tare da amfani da fasaha da bayanan sirri domin gano inda masu garkuwar suke,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa babban burin gwamnati shi ne tabbatar da dawowar Janar Rabe, matarsa da sauran waɗanda ke cikin irin wannan hali cikin ƙoshin lafiya.
Ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da an kamo waɗanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su gaban ƙuliya, yayin da ta buƙaci iyalan waɗanda aka sace da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da fatan alheri a yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da su.
Majiya: Aminiya
