Babban sifeton ƴansandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin ƙara ƙarfafa tsaro a makarantun jihar Katsina, a wani ɓangare na kare ɗalibai da malamai da kuma gine-ginen daga barazanar tsaro.
Babban mataimakin sifeton ƴansandan mai lura da harkokin mulki da kuɗi, DIG Sulaiman Abdul ne ya bayyana haka lokacin wata ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai jihar, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.DIG Abdul ya ce an ɗora wa rundunar yansandan jihar alhakin ƙarfafa sanya idanu da yawaita sintiri a kusa da makarantun jihar, da ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri, da kuma ci gaba da kasancewar jami'an tsaro a harabar makarantun jihar.
Ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin daƙile ayyukan ɓata-gari, da inganta ayyukan kai ɗaukin gaggawa, tare da tabbatar da cewa makarantun sun samu kariya, domin ci gaba da harkokin koyo da koyarwa.
Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
A ƙarshen makon da ya gabata ne tsohon babban janar ɗin sojin Najeriya ya mutu a hannun ƴanbindiga bayan kwashe kwanaki a hannunsu, tare da matarsa, kodayake daga baya jami'an tsaro sun kuɓbutar da matar.