Babbar Kotun Kenya ta umarci gwamnati da ta bayyana cikakkun bayanai game da wata cibiyar killace masu alaƙa da cutar Ebola da ake shirin ginawa tare da tallafin Amurka.
Kotun ta kuma dakatar da duk wani shiri na ci gaba da aikin cibiyar har sai an kammala sauraron ƙarar da aka shigar kan lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa ana shirin gina cibiyar mai gadaje 50 a sansanin sojin sama na Laikipia da ke kusa da garin Nanyuki, domin killace ‘yan Amurka da aka yi zargin sun kamu ko suka yi hulɗa da masu cutar Ebola a Democratic Republic of the Congo da Uganda.
Kungiyar Katiba Institute ce ta kai ƙarar kotu, tana zargin gwamnati da yin yarjejeniyar cikin sirri ba tare da bayyanawa jama’a ba ko samun amincewar majalisa.
Kotun ta ba gwamnati wa’adin kwanaki bakwai ta bayyana duk wata yarjejeniya da aka kulla da Amurka kan cibiyar Ebola ɗin.
Lamarin ya jawo zanga-zanga daga daruruwan mutane a Nanyuki, inda wasu ke nuna damuwa cewa ƙasar Kenya na iya zama wajen killace baƙin ƙasashen waje masu haɗarin kamuwa da Ebola.
Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya kare shirin yana cewa cibiyar za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin kariyar lafiya na ƙasar da kuma shirin tunkarar barkewar cututtuka nan gaba.
Sai dai masu sukar shirin da ƙungiyoyin likitoci sun ce har yanzu akwai tambayoyi masu yawa kan tsaro, shirye-shiryen lafiya, da ikon Kenya na kula da irin wannan haɗarin cuta.