Wata rana Umar (RA) ya na zaune a gidansa a Madina yana jiran isowar wasu shugabannin kabilu da aka mika masa sunayensu domin nada daya daga cikinsu a matsayin gwamna. Sannanne ne cewa ba abu ne mai sauki ka zabi mutumin da zai zama gwamna ba. Koda an san mutum a matsayin gogagge kuma mai basira ba kowane lokaci ba ne za a samu ya hada wadancan halaye da saukin hali da tausayi.
Can kuwa sai daya daga cikin mutanen ya iso cikin kyakkyawar shiga abin burgewa. Ya ce: “Assalamu alaikum warahmatullah.” Umar ya lura yana da alamu irin ta sarakuna kuma ya yi shiga abar yabawa kuma sanye da rawani kyakkyawa.
Amirul Muminina Umar bin Khaddabi ya ce masa ya zauna, kuma bai bata lokaci ba ya zauna a kan tabarma kusa da Umar (RA), ya debi dabino daga cikin wanda aka tanada domin baki ya ci. Bayan tattaunawa da shi na wani lokaci sai Umar (RA) ya gamsu cewa wannan zai iya zama shugaba mai fasaha da wayo wanda ya dace da wannan mukami na Gwamna.
Bayan lokaci kadan da gama tattaunawarsu, sai mutum na biyu ya zo a jigace, ya iso cikin sauri yana neman gafara kan rashin zuwansa a kan lokaci, a yayin da yake karkade kurar da ta mamaye suturarsa da gyara rawaninsa wanda ya karkace zuwa daya daga cikin kunnuwansa. “Ya Amirul Muminina! Ka gafarce ni kan rashin isowa da wuri. A hanyata ta zuwa nan, na hadu da wata tsohuwa ce da jakinta, kafar jakin ta makale a tsakanin wasu duwatsu biyu, ba zan iya wucewa ba ba tare da na taimaka mata ba, ina tabbatar maka aiki ne mai wahala, don haka ina jin tsoro domin na dan makara.”
Umar (RA) ya karbi neman afuwarsa sannan ya nuna masa cewa ya kwantar da hankalinsa, yayin da abokin takararsa yaji sai ya yi dariya ya ce, “To yanzu in tambaye ka wanne ne ya fi muhimmanci, kujerar gwamna ko kafar jakin?”
A daidai wannan lokaci sai daya daga cikin ’ya’yan Sayidina Umar (RA) ya fito da gudu daga daki ya fada ka cinyoyin Umar (RA). Sai Umar (RA) ya rungume shi da hannuwansa ya sumbace shi har sau biyu a kansa.
Mutum na farko sai ya gaza boye rashin jin dadinsa da ganin haka. Sai ya ce: “Ban taba yin haka ba ya Amirul Muminina. ’Ya’yana goma ba su ma isa su zo kusa da ni ba, kuma hakika ban taba sumbatarsu ba.”
Umar (RA) ya zuba wa mutumin nan ido ya kada kansa, sannan ya ce: “Babu wani abu da zan iya yi a kan ka, idan Allah ya kekasar da zuciyarka ta ki yin kirki. To amma ka tuna Allah yana tausaya wa wanda ya nuna tausayi ga halittunsa.”
Sai kuma Umar ya lura mutum na biyu yana murmushi tare da jin kunya, sai ya tambaye shi abin da ya faru.
Sai mutumin ya ce: “Ka gani ya Amirul Muminina! Ina da matsala sabanin haka. Ina da ’ya’ya biyar amma a koyaushe suna fado min a jiki. Kafin ma in taho karamarsu mai suna Laila ba ta so in taho ba, ta yi ta makale min tana bukatar in dauke ta, wannan ne ya sa ta bata min riga da kura.”
Sai Umar (RA) ya yi murmushi ya kalli sakatarensa wanda ke jirar ya ji daga Umar (RA) wane mutum ne ya yanke shawara ya ba shi gwamna. Sai Sayyidina Umar (RA) yace: “Rubuta wa wannan mutum na biyu wasikar nada shi Gwamna, ina da yakinin shi ne ya dace da wannan aiki.
Mutumin nan na farko na jin shawarar da Umar (RA) ya yanke, nan take ya tarin bakin ciki ya turnuke shi. Sai Umar (RA) ya ce da mutumin nan na farko: “bai zai yiwu ka zama shugaba ba, kana mutum mai alfahari. Shugaban kabilar da zai zama gwamna ya kamata a ce yana da tausayi, kuma za a so ya dauki lokaci yana taimakon wasu. Wannan mutum na biyu mutumin kirki ne, kuma tunda ya zo nan yake nuna min yana da wadannan halayen kirki biyu.”
Mutum na farko wanda da kyar ya iya dakatar da tarin da yake yi, ya yi ta kokarin ya gano abin da Umar (RA) yake magana a kai, amma tunda Allah ya takura zuciyarsa haka ya tafi ba tare da ya fahimci ko da abu daya ba, abinda ya sanya a ransa ita ce kujerar gwamna.
Don haka Sayyidina Umar (RA) ya ba da mukamin gwamna ga mutumin da ya zo da riga mai kura wanda ya damu da yara da jakuna da tsofaffin mata.
