BUA Ya Musanta Rahoton Sayen Kaso 70 Cikin 100 Na Kano Pillars

Kamfanin BUA Group ya musanta rahotannin da ke cewa shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu, ya gabatar da tayin sayen kaso 70 cikin 100 na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

BUA Group

A wata sanarwa da mahukuntan kamfanin suka fitar a ranar Litinin, BUA ya bayyana cewa babu gaskiya a rahoton, yana mai jaddada cewa kamfanin ko shugabansa ba su taɓa gabatar da irin wannan tayi ba, kuma ba su shiga wata tattaunawa da kowa kan batun ba.

Kamfanin ya ce rahoton ba shi da tushe balle makama, tare da yin kira ga jama'a da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da shi.

BUA ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da jama'a su riƙa dogaro da sanarwar da ake fitarwa ta hanyoyin sadarwa na hukuma na kamfanin wajen tabbatar da duk wani bayani da ya shafi ayyukansa.

Kano Pillars, wadda aka fi sani da "Sai Masu Gida", na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafiya tarihi a Najeriya, kuma Gwamnatin Jihar Kano ce ke da mallakarta tare da ɗaukar nauyin tafiyar da ita.

Abdul Samad Rabiu, ɗan asalin Jihar Kano ne, kuma yana cikin attajiran Afirka mafiya arziki, inda mujallar Forbes ta kiyasta darajar dukiyarsa ta haura dala biliyan 14.

Post a Comment

Previous Post Next Post