Wasu muhimman bayanai da hotuna da suka shafi wayar Apple iPhone 18 Pro sun bayyana bayan wani hari ta yanar gizo da aka kai kan Tata Electronics, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke haɗa na'urorin Apple a Indiya.
Rahotanni sun ce masu kutse sun sace takardu masu muhimmanci da suka haɗa da jerin masu samar da kayayyakin iPhone 18 Pro, bayanan sassan wayar, taswirar kayan haɗi, da hotunan gwajin faɗuwar wayar (drop tests) kafin a fitar da ita kasuwa.
Masana sun ce wannan na ɗaya daga cikin manyan bayanan sirri da suka taɓa tonuwa game da tsarin samar da iPhone, domin Apple kan ɓoye bayanan masu samar mata da kayayyaki da kuma tsarin kera sabbin na'urorinta.
Har yanzu Apple da Tata Electronics ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, amma rahotanni sun nuna cewa ana gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan ƙarfafa tsaro domin hana sake faruwar irin wannan kutse.
Masana tsaro sun yi gargadin cewa irin wannan kutse na iya shafar sirrin kasuwanci da tsarin samar da kayayyaki na Apple, duk da cewa babu wata shaida da ke nuna cewa bayanan masu amfani da iPhone sun shiga hannun masu kutse.