Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya, musamman jami'an aikin soji na musamman na Hadin Kai bisa ceto mutum 360 da aka sace a jihar daga tsaunin Mandara.
Tsaunin Mandara na daga cikin fitattun maɓoyar mayaƙan Boko Haram da ke da tsananin haɗari a kudancin jihar Borno.A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana ceto mutanen na Ngoshe a matsayin babbar nasara.
Ya ce nasarar za ta ƙara taimakawa wajen kwantar da hankalin ƴan ƙasar, musamman ƴan jihar a kan ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da tsaro.
"Ina godiya ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da babban hafsan tsaron Najeriya da babban hafsan sojin ƙasa da kwamandan sojojin Borno da sojojin baki ɗaya bisa ƙoƙarin da suka yi."