Gwamnatin Jihar Katsina Ta Musanta Zargin Daukar Nauyin Aikin Hajjin Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta zargin cewa ta dauki nauyin aikin Hajjin shugabannin ’yan bindiga da wasu masu aikata laifuka, tana mai bayyana zargin a matsayin karya, da kuma yaudara mai ɗauke da manufar siyasa.

Dikko Umar Radda

Martanin gwamnatin ya biyo bayan kalaman da Bashir Kurfi ya yi a wani shiri na Trust TV, inda ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta tura wasu masu hannu a ta’addanci zuwa aikin Hajji.

A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na jihar, Dakta Nasir Mu’azu, ya fitar, gwamnatin ta ce zargin ba shi da wata hujja ko tushe na gaskiya.

Gwamnatin ta ce irin waɗannan kalamai na iya raunana ƙoƙarin da take yi tare da jami’an tsaro wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Ta kuma bayyana cewa ana yaɗa irin waɗannan zarge-zarge ne a daidai lokacin da ake samun nasarori a yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Gwamnatin ta zargi wasu mutane da amfani da batun tsaro domin cimma muradun kansu na siyasa da na kashin kai.

Haka kuma, ta ƙalubalanci masu wannan zargi da su gabatar da sahihan hujjoji da za su tabbatar da ikirarinsu, tare da gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar matakin shari’a idan aka kasa gabatar da hujjoji.

A ƙarshe, gwamnatin ta buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da zarge-zargen tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post