Gwamnatin Tarayya Ta Soke Hutun Watanni Uku Na Kafin Ritaya Ga Ma'aikatan Gwamnanti

Gwamnatin Tarayya ta umarci daukacin ma’aikatu, hukumomi, da sassan gwamnati (MDAs) da su gaggauta dakatar da dabi'ar tura ma'aikatan gwamnati hutun tilas na watanni uku kafin su yi ritaya. Gwamnatin ta bayyana cewa babu irin wannan tanadi a cikin Kundin Dokokin Ma'aikatan Gwamnati (PSR).

Wannan umarni yana kunshe ne cikin wata wasika da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta aike wa manyan jami’an gwamnati, da suka hada da ministoci, manyan sakatarori, shugabannin tsaro, da shugabannin hukumomi daban-daban.

A cikin takardar mai taken “Fassarar Da Ta dace Kan Dokar Ma’aikatan Gwamnati Lamba 120243 Game da Al’amuran Kafin Ritaya,” Shugabar Ma’aikatan ta bayyana cewa hukumomi da dama sun dade suna fassara lokacin sanarwar ritaya a matsayin lokacin hutu na atomatik. Ta kara da cewa wannan kuskure ne da ke janyo janye jami'ai daga bakin ayyukansu tun kafin lokacinsu na cika.

A cewar Walson-Jack, abin da dokar ma’aikatan gwamnati ta nema kawai shi ne; ma’aikacin da ya isa lokacin ritaya ya bayar da sanarwar barin aiki ta watanni uku, sannan ya halarci bitar shiga ritaya ta wata guda, sannan ya yi amfani da sauran lokacin wajen gyara takardunsa na aiki da na fansho.

"Wannan da ake kira 'hutun tilas na watanni uku kafin ritaya' ba shi da wani kwararan hujjoji ko tushe a cikin Kundin Dokokin Ma’aikatan Gwamnati," in ji Walson-Jack.

Yadda Tsarin Watanni Ukun Yake A Ka'ida

Hukumar ta fayyace cewa Dokar PSR 120243 ta gina abubuwa guda uku mabanbanta wadanda ya kamata ma'aikaci ya cika cikin watanni ukun:

  1. Wata Na Farko: Ma'aikaci zai bayar da takardar sanarwar ritaya, sannan zai halarci taron bita ko kwas na musamman na tsawon wata guda domin shirin kalubalen rayuwa bayan aiki.

  2. Wata Na Biyu Da Na Uku: Ma'aikaci zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum yayin da yake amfani da sauran lokutan wajen tantancewa da kammala rajistar takardunsa na fansho da na tsawon shekarun aiki.

Sanarwar ta nanata cewa, jami’in da ke shirin ritaya ya kasance ma’aikacin gwamnati mai cikakken iko a cikin daukacin tsawon watanni ukun na sanarwa. Don haka, ana sa ran zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na hukuma, sai dai idan yana halartar bitar ritaya da aka amince da ita, ko kuma idan an ba shi damar hutu ta hanyar amfani da wasu ka'idoji na daban na hutun shekara-shekara.

Sakamakon haka, an umarci daukacin hukumomin gwamnati da su daina tilasta wa ma’aikata barin mukamansu kafin ranar ritayarsu ta gaskiya.

A karkashin wannan sabon tsari, ya zama wajibai ga ma'aikatu da hukumomi su tabbatar da cewa ma'aikatan da ke shirin ritaya sun ci gaba da sauke nauyin da ke kansu, sun shiga cikin shirye-shiryen bitar ritaya, sannan sun kammala daidaita bayanan ayyukansu da na fansho kafin su fice daga aikin gwamnati na din-din-din.

Post a Comment

Previous Post Next Post