A Cikin Kwanakin Da Ba Su Wuce 21 'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutane 29 da Jikkata 10 Tare Da Yin Garkuwa Da 3 A Karamar Hukumar Matazu

Daga ranar 9/05/2026 zuwa ranar 30/05/2026 al'ummar ƙaramar hukumar Matazu musamman daga gundumar Sayaya da Kogari da Madobi da kuma garin matazu, jagoran 'yan bindiga Kachalla Muhammadu ya kashe aƙalla mutane ashirin da tara (29) da jikkata goma (10), tare da yin garkuwa da 3, a cikin kwanakin da ba su wuce ashirin da ɗaya (21) ba.

A ƙasa ga jerin sunayen garuruwan da aka hare-haren da kuma adadin mutanen da aka kashe da kuma adadin waɗanda aka ji wa ciwo suke jinya.

A ranar 9 ga watan Mayu, na wannan shekarar 2026 'yan bindiga sun shiga ƙauyan Kukan Damisa da ke gundumar Sayaya inda suka kashe mutane bakwai (7) tare da jikkata mutum ɗaya (1).
A ranar 10 ga watan Mayu ɗin dai suka shiga ƙauyen Dugul da Hayin Nomau da ke gundumar Mazoji, inda suka kashe mutane 9 tare da jikkata mutane 4.
Haka nan, a ranar 25 ga watan Mayu ɗin dai suka sake shiga garin Dugul suka kashe mutane 4 tare da jikkata mutum ɗaya.
Har wa yau, ɓarayin dajin sun shiga Gidan Mamuda da yake gundumar Kogari a ranar 25 ga watan Mayu, inda suka kashe mutane 2 tare da jikkata mutum ɗaya.
Kwana biyu da faruwar wannan, ranar 27 ga watan Mayu, ɓarayin daji sun shiga ƙauyen Gidan Baruma da yake gundumar Saya, inda suka kashe mutum ɗaya (1).
Sai kuma ranar 28/05/2026 suka shiga cikin garin Sayaya suka kashe mutane uku har lahira.
A ranar 29 ga Mayu ɓarayin daji sun tare mutanen da suka je sharar gona a garin Matazu inda suka kashe mutane 2 tare da jikkata mutane 2. 
Haka nan, a ranar dai ta 29/05 suka kuma shiga garin Sayaya inda a nan ma suka kashe masu sharar gona mutum ɗaya (1).
Sai kuma ranar 30/05/2026 ɓarayin dajin ƙarƙashin ikon Kachalla Muhammadu suka tare hanyar Matazu suka sace mutane 3 daga cikinsu akwai Manjo Janar Rabe Abubakar da matarsa Hajiya Amina Abubakar da kuma direbansa mai suna Abdullahi Sa'idu wanda daga bisani suka saki direban motar.

Post a Comment

Previous Post Next Post